Kamfanin NPDC na samar da gangar mai dubu 205 kowace rana
Ministar Man Fetur Misis Diezani Alison-Madueke ta bayyana cewa a yanzu Kamfanin Mai na NPDC na samar da gangar danyen mai dubu 205, 007 a kowace rana sabanin a baya da yake samar da gangar danyen mai dubu 130 kowace rana. Ministar ta ce wannan yana da cikin shirin kasar nan na samar da gangar […]

Ministar Man Fetur Misis Diezani Alison-Madueke ta bayyana cewa a yanzu Kamfanin Mai na NPDC na samar da gangar danyen mai dubu 205, 007 a kowace rana sabanin a baya da yake samar da gangar danyen mai dubu 130 kowace rana.
Ministar ta ce wannan yana da cikin shirin kasar nan na samar da gangar danyen mai miliyan 2.24 kowace rana duk da matsalolin da ake fama da su wadanda suka hada da satar mai da fasa bututun mai.
Ta ce NPDC zai ci gaba da jajircewa wajen ganin ya samar da man da zai wadatar da kasuwar cikin gida, inda ta tabbatar da cibiyar Oredu da ta Ughelli da Utorogu na samar da iskar gas mai yawan kibuki miliyan 600, wanda hakan babbar nasara ce ga ma’aikatarsu.
Ministar ta bayyana haka ne a lokacin da take jawabi a kan kasafin kudi na bara (2014) da kuma na bana (2015) a gaban kwamitin majalisar wakilai a kan albarkatun man fetur da ake hakowa a teku da kuma na tudu.
Madueke ta yi alkawarin ma’aikatarsu za ta samar da karin hanyoyin samar da kudin shiga da suka hada da bunkasa harkokin iskar gas da inganta matatun mai da kuma magance bin duk wadansu hanyoyin da za su jawo asara.
Ta tabbatar da cewa ma’aikatarsu ta zage damtse wajen saka hannu jari don samar da kudin shiga a bangaren man fetur a shekarar 2015.