Kamfanin NTM ya karrama kwastomomi a Kano
Kamfanin da ke hada motoci na NTM da ke Kano ya karrama manyan kwastomominsa uku don nuna musu godiyarsa sakamakon huldar kasuwanci suke yi da shi. A lokacin da yake jawabi a dakin taro na kamfanin NTM, Manajin-Daraktan kamfanin Ibrahim dalhatu Bayero ya ce kamfaninsu da ke Kano na daya daga cikin manyan kamfanonin da […]
Kamfanin da ke hada motoci na NTM da ke Kano ya karrama manyan kwastomominsa uku don nuna musu godiyarsa sakamakon huldar kasuwanci suke yi da shi.
A lokacin da yake jawabi a dakin taro na kamfanin NTM, Manajin-Daraktan kamfanin Ibrahim dalhatu Bayero ya ce kamfaninsu da ke Kano na daya daga cikin manyan kamfanonin da ke hada ababen hawa a Najeriya.
Ya ce Bayan gwamnatin tarayya ta hada gwiwa da kamfanin FIAT IBECO na kasar Italiya ce ta kirkiro kamfanin NTM a shekarar 1975, don kerawa da kuma hada manyan motoci da taraktoci.
“Kamfanin NTM ya fara gudanar da ayyukansa na hada manyan motoci da taraktocin noma a shekarar 1980, inda aka rufe shi a shekarar 1987 saboda matsalar kudi. Bayan komai ya daidai ne NTM ya hada kai da wani fitaccen kamfanin kera motoci, inda aka yi yarjejeniyar wannan kamfanin zai rika taimaka mana kan yadda za mu rika hada ababen hawa da kera su da sayar da su da gyara su da kuma horar da ma’aikatanmu.” Inji Bayero.
A wurin taron Sarki Kano Muhammad Sanusi na II ya ce kamfanin ya cancanci a yaba masa bisa ga yadda yake gudanar da ayyukan duk da tabarbarewar tattalin arziki.
Kwastomomin da kamfanin ya karrama sun hada kamfanin mai na Ammasco Oil da Hukumar Tsabtace Muhalli ta Jihar Kano (REMASAB) da kuma Kamfanin Sharubutu Enterprises, Kano.