‘Kamfanin Obasanjo na cikin kamfanoni 1901 da suka ki biyan haraji’
Hukumar Tattara Kudaden Haraji ta Kasa (FIRS) ta wallafa sunayen wasu kamfanoni da ba sa biyan kudaden haraji da doka ta tanada. Sunayen dai sun kunshi kamfanoni da suke harkokin kasuwanci guda 1901, wadanda hukumar ta wallafa a shafinta na Intanet mai taken ‘Consolidated Tad Defaulters list’ wato sunayen wadanda suka ki biyan haraji. Jerin […]
Hukumar Tattara Kudaden Haraji ta Kasa (FIRS) ta wallafa sunayen wasu kamfanoni da ba sa biyan kudaden haraji da doka ta tanada. Sunayen dai sun kunshi kamfanoni da suke harkokin kasuwanci guda 1901, wadanda hukumar ta wallafa a shafinta na Intanet mai taken ‘Consolidated Tad Defaulters list’ wato sunayen wadanda suka ki biyan haraji.
Jerin sunayen da aka wallafa a shafi 586, ya kunshi kamfanonin da suka hada da na tsohon Shugaban Kasa Cif Olusegun Obasanjo mai suna Obasanjo Farms Nig. limited da Feedmill Coldstone Creamery Limited da ke Yaba da Grand Skuare Supermarket and Stores da Slot Enterprises da cocin Assemble of God Nigeria da Payporte Technology Limited da Dabido Music Worldwide Limited da United Capital Plc.
Ragowar sun hada da Birgin Oil Limited da asibitin Nizamiye Hospital da Tesco Ekuipments Nigeria Limited da Marine Golf Shipping da sauransu.
Shugaban Hukumar FIRS, Babatunde Folwer ya bayyana wasu daga cikin kamfanonin da suke cikin wannan matsala cewa suna sanya ido a asusun ajiyarsu na banki karkashin dokar a rike asusun har sai kamfanonin sun biya basussukan kamar yadda sashi na 31 na Dokar FIRS ya tanada cewa duk kamfanin da bai gyara matsalar harajinsa da hukumar ba ya gaggauta gyaran kafin nan da kwana 30, ko hukumar ta yi amfani da sashi na 49 (2) na dokar da ta ba ta ikon tillasta musu biya da karfi.
“Saboda a kauce wa wannan matsalar hukumar ta shawarci daraktoci da manajoji da sakatarorin kowane kamfani su tabbatar sun bi umarnin wannan hukuma kafin ta yi amfani da ikon da doka ta bayar na hukunta duk wanda ya saba ka’ida,” inji shi.