Kamfanin Royal Ceramics ya kudiri aniyar daukaka kayayyakin gida Najeriya

A ci gaba da kokarin daukaka kayyakain da ake sana’antawa a nan  Najeriya da amfani da su, kamfanin West African Ceramics Limited ya kaddamar da manyan shagunan sayar kayan ginin da aka hada a Najeriya a Kaduna da Babban Birnin Tarayya, Abuja. kaddamar da shagunan kayayyakin wanda shi ne karo na 7 da na 8 […]

Kamfanin Royal Ceramics ya kudiri aniyar daukaka kayayyakin gida Najeriya

A ci gaba da kokarin daukaka kayyakain da ake sana’antawa a nan  Najeriya da amfani da su, kamfanin West African Ceramics Limited ya kaddamar da manyan shagunan sayar kayan ginin da aka hada a Najeriya a Kaduna da Babban Birnin Tarayya, Abuja.

kaddamar da shagunan kayayyakin wanda shi ne karo na 7 da na 8 da kamfanin ke kaddamar irin wannan  tun lokacin da ya fara harka a Najeriya.

Ta hanyar hulda da abokan ciniki da kyau, kamfanin ya samu damar kafa sassa a duk manyan biranen Najeriya, wadanda suka hada da Sharada da ke Kano da Mile 12 da Fatakwal da Maraba a Jihar Nasarawa da Jos da Osogbo da Enugu. Sannan sun hada hannu da kamfanin Arda Integrated Ceramics na Kaduna, wanda shi ma wani babban kamfanin kayayyakin gini ne da ke kan titin Ahmadu Bello a cikin garin Kaduna, sannan kuma suna hadin gwiwa da kamfanin JCA Global Consultant da ke Abuja.

Da yake jawabi, babban manajan kamfanin, Mista Bhaskar Rao ya ce, “Babban makasudin bude wadannan shaguna shi ne tallafa wa kokarin gwamnati na ganin cewa ana amfani da kayayyakin da ake sana’antawa a cikin gida ta hanyar raba kayan yadda ya kamata yadda za a same su a ko’ina a fadin kasar nan, kuma cikin sauki da rahusa, inda hakan ne zai sa abokan ciki su ci gaba da saya.”

Babban Jami’in Gudanarwa na Kamfanin Arda Integrated Ceramics, Mista Arthur Atuka,  ya ce burin wannan gwamnati na habbaka bangaren kasuwanci da kuma kamfanonin cikin gida ba zai  ciki ba har sai an rika amfani da kayayyakin da ake sana’antawa a cikin gida sama da wadanda ake shigowa da su. Sannan babban jami’in gudanarwa kuma Shugaban Kamfanin JCA Consultant Ltd, Chief Kachi Iheme, ya bukaci mutane da su rika amfani da kayayyakin da aka sana’anatawa a gida domin karfafa wa kamfanonin.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno