Kamfanin Samsung ya kaddamar da sabuwar waya
Kamfanin Samsung ya fara sayar da sabuwar wayar da ya bullo da ita mai amfani da manhajar Tizen a kasar Indiya a makon jiya. An fara sayar da wayar Z1 a India a kan Dala 92 (kimanin Naira dubu 17), kuma a cewar kamfanin Samsung, wayar tana saurin wartsakewa idan an kunna ta, sannan batirinta […]

Kamfanin Samsung ya fara sayar da sabuwar wayar da ya bullo da ita mai amfani da manhajar Tizen a kasar Indiya a makon jiya.
An fara sayar da wayar Z1 a India a kan Dala 92 (kimanin Naira dubu 17), kuma a cewar kamfanin Samsung, wayar tana saurin wartsakewa idan an kunna ta, sannan batirinta yana dadewa kafin ya yi sanyi.
A kwanakin baya kamfanin Samsung ya dakatar da shirinsa na fara sayar da sabuwar wayar a kasashen Rasha da Japan.
Wani kwararre a fannin fasaha ya ce fara sayar da wayar a Indiya wani mataki ne na fara kaurace wa wayoyin manhajar Android.
Ben Wood na cibiyar tuntuba kan sha’anin fasaha ta CCS Insight ya ce “idan aka kwatanta, wayar Tizen tafi ta Android karfin batiri”.
Ya zuwa yanzu, kamfanin Samsung shi ne ke kan gaba a duniya wajen samun cinikin wayoyin Android. Kuma wayar Tizen tana da na’urar daukan hoto daga baya mai karfin pidel 3.1, sannan daga gaba mai karfin pidel 0.1, sannan kuma tana amfani da layi biyu. Kamfanin ya ce wayar Z1 tana bude shafukan intanet da sauri fiye da sauran wayoyi masu farashi iri daya da ita.