Kamfanin Samsung ya kirkiro shirin horar da Injiniyoyi
Kamfanin Samsung na Yammacin Afirka ya kirkiro shirin horar da injiniyoyi a kasar nan. Kamfanin ya bayyana hakan ne a Abuja a ranar Talata a lokacin da ya cimma yarjejeniya da kungiyar Injiniyoyi ta Najeriya.Yarjejeniyar ta nuna kungiyar injiniyoyin za su rika tallata hajar kamfanin, inda kamfanin zai rika horar da mambobin kungiyar don su […]

Kamfanin Samsung na Yammacin Afirka ya kirkiro shirin horar da injiniyoyi a kasar nan.
Kamfanin ya bayyana hakan ne a Abuja a ranar Talata a lokacin da ya cimma yarjejeniya da kungiyar Injiniyoyi ta Najeriya.
Yarjejeniyar ta nuna kungiyar injiniyoyin za su rika tallata hajar kamfanin, inda kamfanin zai rika horar da mambobin kungiyar don su samu kwarewar da ake bukata.
Shugaban kungiyar Ademola Isaac Olorunfemi ya jagoranci ’yan kungiyar, shi kuma ya sanya hannu a yarjejeniyar, inda kuma Manajin-Daraktan Kamfanin na Yammacin Afirka Brabo Kim ya sanya wa kamfanin hannu.
Shugaban kungiyar ya ce “Mun bukaci kamfanin ya rage farashin kayayyakinsa, sannan ya samar da shirin da zai rika horar da mambobinmu, sannan ya biya kungiya Naira miliyan 15.”
Kamfanin ya ce “Muna tsammanin kungiyar za ta rika tallata hajar kamfaninmu a shafinta na intanet, ta kuma bayyana wa mutane ingancin kayayyakinmu, sannan ta ba mu damar baje-kolin hajarmu a duk wani biki ko taron da suka shirya.”
Shugaban kungiyar ya ce wannan yarjejeniyar za ta kasance babbar tarihi, ba za su saba abubuwan da suka cimma yayin yarjejeniyar ba.
Ya ce: “Za mu tallata musu hajarsu, sannan mu nemi yarjejeniyar ta zama ta dindindin, mun yi farin ciki sosai.”