Kamfanin Saudiyya ya haɗa kai da gwamnatin Jigawa kan noman dabino

Kasar Nijeriya na samar da kusan tan 21,000 na dabino a kowace shekara, inda Jihar Jigawa ke cikin jihohi mafi girma wajen samar da dabino.

Kamfanin Saudiyya ya haɗa kai da gwamnatin Jigawa kan noman dabino

Dabino

Samar da dabino zai samu sauyi mai mahimmanci a Jihar Jigawa bayan da wani kamfani daga kasar Saudiyya mai samar da dabino da gwamnatin jihar suka ƙulla yarjejeniya domin ƙara yawan amfanin gona.

Ta wannan haɗin gwiwa za a kawo sababbin fasahohin zamani da irin dabino masu yawa don shigar da su cikin tsarin noma.

A cewar bayanai daga Hukumar Abinci da Aikin Noma ta Majalisar Ɗinkin Duniya (FAO), Saudiyya ita ce ƙasa ta biyu mafi girma wajen samar da dabino na duniya, inda take samar da tan miliyan 1.61 na dabino.

Masar ita ce ƙasa mafi girma wajen samar da dabino, inda ta noma tan miliyan 1.73 na dabino a shekarar 2022, yayin da Aljeriya ke matsayi na uku da tan miliyan 1.25.

Haɗin gwiwar Gwamnatin Jihar Jigawa da wannan rukunin daga Saudiyya tare da Netay Agro-Tech, wani kamfanin amfani da ke Nijeriya ma gudanar da harkokin noma, zai kawo karuwar samuwar dabino a jihar.

Kasar Nijeriya na samar da kusan tan 21,000 na dabino a kowace shekara, inda Jihar Jigawa ke cikin jihohi mafi girma wajen samar da dabino.

Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi, yayin da yake jawabi lokacin da ya karɓi wata tawaga daga babban kamfanin noma na Saudiyya, wanda ya ƙware wajen shuka dabino da sarrafa gonaki a ofishinsa da ke Dutse, ya ce wannan haɗin gwiwa zai kawo sabon salo ga samar da dabino a Jigawa.

Gwamnan ya bayyana goyon bayan gwamnatinsa ga wannan yunƙuri, yana mai cewa ya dace da ajandar bunkasa aikin gona ta jihar.

“Mun yi maraba da zuwanku Jihar Jigawa tare da nuna godiya ga sha’awar da kuka nuna wajen yin aiki tare da mu.

“A matsayinmu na gwamnati, mun jajirce kan wannan haɗin gwiwa saboda zai amfani al’ummarmu sosai.

“Zuwanku da sha’awar yin haɗin gwiwa da mu wajen kafa gonakin dabino a fadin jihar, da kuma inganta samar da alkama, sun yi daidai da burinmu na bunkasa aikin noma,” in ji gwamnan.

Ya sake jaddada shirinsa na samar da dukkan kayan aiki da ake bukata don tabbatar da nasarar aiwatar da wannan shiri.

Ya bayyana kwarin gwiwa cewa, haɗin gwiwar zai samar da fa’idodi masu ban mamaki tare da mayar da Jigawa ta zama jagora a masana’antar dabino ta duniya.

Shugaban tawagar, Abdul’aziz Abdurrahman-Al-Awf ya jaddada ƙudurinsu na kawo fasahohin noma na zamani zuwa Jihar Jigawa.

“Muna son tabbatar da samar da dabino a duk shekara, ba wai kawai a wasu yanayi ba, kuma haɗin gwiwarmu zai haɗa da horar da manoma da ba wa matasa dama,” in ji shi.

 

Dangote ya rage farashin man fetur zuwa N825 a Legas

Na gaji bashin 8.9bn a matsayin shugaban APC — Ganduje

Boko Haram sun sace mutum 2 da kayan abinci a Borno

Buhari da El-Rufai ba su halarci babban taron APC ba