Kamfanin Shell zai biya diyyar Dala miliyan 84
A shekaranjiya Laraba ne kamfanin mai na Shell da ke aikin hako mai a kasar nan ya amince ya biya diyyar Dala miliyan 84 ga al’ummar da malalar mai ta shafa a yankin Naija-Delta da ke kudancin kasar nan. An cimma wannan yarjejeniya ne bisa sulhuntawar da aka yi a wajen kotu, bayan da wasu […]
A shekaranjiya Laraba ne kamfanin mai na Shell da ke aikin hako mai a kasar nan ya amince ya biya diyyar Dala miliyan 84 ga al’ummar da malalar mai ta shafa a yankin Naija-Delta da ke kudancin kasar nan.
An cimma wannan yarjejeniya ne bisa sulhuntawar da aka yi a wajen kotu, bayan da wasu lauyoyi a birnin Landan suka karbi shari’ar. Kuma za a raba diyyar ce kamar haka: masunta da manoma da matsalar malamar ta shafa za su samu Dala dubu uku kowannensu, yayin da kaso mai tsoka na kudin za a bai wa al’umar yankin Bodo. Har ila yau, al’ummar yankin Ogoni ma sun samu wani abu daga diyyar.
Sulhun da aka cimma shi ne mafi girma irinsa a Najeriya, kuma ya kawo karshen shari’ar da aka shafe shekara uku ana yi. Masu rajin kare al’ummomin Bodo sun ce kamata ya yi tun farko kamfanin ya amsa laifinsa, amma sai ya yi kimeme.
Kodayake, kamfanin ya dage cewa malalar mai da ya jawo gurbacewar muhalli a yankin, ya faru ne saboda yadda al’ummar yankin suke satar danyen man da kuma aikace-aikacen matatun man bayan fage.