Kamfanin Shell zai sanya hannun jarin Dala biliyan 15 a Najeriya-Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari ya ce kamfanin mai na Shell yana shirye-shiryen sanya hannun jarin Dala miliyan 15 a Najeriya. Shugaban ya bayyana haka ne a taron kasashen rainon Ingila kan kasuwanci da aka yi a Landan inda ya bakuci samun alakar harkokin kasuwanci tsakanin kasashen rainon Ingila. “Kafin na zo nan taron kamfanin […]
Shugaba Muhammadu Buhari ya ce kamfanin mai na Shell yana shirye-shiryen sanya hannun jarin Dala miliyan 15 a Najeriya.
Shugaban ya bayyana haka ne a taron kasashen rainon Ingila kan kasuwanci da aka yi a Landan inda ya bakuci samun alakar harkokin kasuwanci tsakanin kasashen rainon Ingila.
“Kafin na zo nan taron kamfanin Shell sun zo sun gana da ni suna shirye-shiryen sanya hannun jari da ya kai na Dala biliyan 15 a Najeriya. Sun zo sun fada mini labarin”. Inji shi
Da yake jawabi a wurin taron, Shugaban ya ce “Ya zama wajibi kasashen rainon Ingila su kaucewa rikici a kasuwanci sannan kuma ya zama wajibi su yi aiki tare don kare martabar dokokin kasuwanci duniya”
A wata sanarwar da mai magana da yawunsa ya sanyawa hannu, Mista Femi Adesina ya bayyana cewa shugaban kasar ya kalubalanci membobin kungiyar kasashen rainon Ingila su bayar da goyon baya kan hadin kan kasashen.