Kamfanin siminti na Ashaka zai fadada ayyukansa a bana
A kokarinsa na fadada ayyukansa da kuma kara sama wa jama’a aiki, Kamfanin Siminti na Ashaka ya yi shirin kashe Naira biliyan 229 wajen fadada kamfanin.A cikin wata sanarwa daga shugaban kamfanin Lafarge a Najeriya da kasar Benin, Mr. Guillaume Roud ya bayyana cewa aikin zai dauki tsawon wata 36 kafin a kammala shi kuma […]
A kokarinsa na fadada ayyukansa da kuma kara sama wa jama’a aiki, Kamfanin Siminti na Ashaka ya yi shirin kashe Naira biliyan 229 wajen fadada kamfanin.
A cikin wata sanarwa daga shugaban kamfanin Lafarge a Najeriya da kasar Benin, Mr. Guillaume Roud ya bayyana cewa aikin zai dauki tsawon wata 36 kafin a kammala shi kuma idan aka gama zai kara yawan simintin da yake samarwa a kowace rana, sannan kuma ya kara yawan ma’aikata da zai dauka don yin aiki a kamfanin.
Shugaban ya kuma tabbatar wa da al’ummar Ashaka cewar yankin Arewa-Maso-Gabas da kuma Najeriya gaba daya, cewa kamfanin zai ci gaba da tallafa wa al’ummomin wannan yankin da ayyukan rowan sha, makarantu da koyar da sana’o’i da ba da tallafin karo karatu ga daliban yankin don bunkasa ilmi. Haka kuma ana sa ran injinan da ake bukata don wannan aiki za su fara isowa kasar nan, nan da mako biyu kuma da zarar sun iso za a fara aikin gadan-gadan. Daga karshe shugaban ya nemi hadin kai da goyon baya daga al’ummar wannan yanki.