Kamfanin Simintin dangote ya kafa rassa a Senegal da Kamaru

Kamfanin simintin dangote ya bayyana cewa ya kafa rassa a kasar Senegal da Kamaru, sannan ya samu ribar Naira biliyan 159. Kamfanin ya bayyana a yanzu wadannan rassan nasa tuni suka fara gudanar ayyukansu a wadannan kasashen.Kamfanin ya kuma bayyana a watan gobe kamfanonin simintinsa da ke Habasha da Zambiya za su fara gudanar da […]

Kamfanin Simintin dangote ya kafa rassa a Senegal da Kamaru
Kamfanin Simintin dangote ya kafa rassa a Senegal da Kamaru

Kamfanin simintin dangote ya bayyana cewa ya kafa rassa a kasar Senegal da Kamaru, sannan ya samu ribar Naira biliyan 159.

Kamfanin ya bayyana a yanzu wadannan rassan nasa tuni suka fara gudanar ayyukansu a wadannan kasashen.
Kamfanin ya kuma bayyana a watan gobe kamfanonin simintinsa da ke Habasha da Zambiya za su fara gudanar da ayyukansu.
Sabon kamfanin simintin dangote da ke kasar Senegal yana Gundumar Pout mai nisa Kilomita 75 daga Dakar babban birnin kasar, inda ya kamfanin ya bayyana cewa zai samar da guraben ayyuka 1,000, sannan zai rika samar da tan miliyan 1.5 na siminti kowace shekara, wanda hakan ya nuna za a samu karuwar fiye da tan miliyan daya na siminti a kasar, musamman ma da kasar take bukatar fiye da tan miliyan 2 na siminti kowace shekara, inda ta dogara da kasar Mali wajen shigo da siminti kasar.
Shugaban sashin masana’antu na Kamfanin dangote a Senegal, Luk Haelterman ya bayyana kamfanin ya zuba jarin Dala miliyan 300 a kamfanin simintin kasar.
A rahoton da kamfanin ya fitar a ranar 31 ga Dismaba, 2014 ya bayyana ya samu ribar Naira biliyan 159.5.
Babban Daraktan kamfanin Mista Debakumar Edwin ya ce: “Ina mai alfaharin sanar da cewa mun kaddamar da samar da sminiti tan miliyan 9 na daga kamfanin siminti na Obajana da kuma Ibese. Burinmu mu samar da babban kamfanin siminti a duniya. A ketare mun bude kamfanin siminti a Afirka ta Kudu da kuma Senegal cikin shekarar 2014, sannan ga kuma Kamaru da Zambiya, sannan Habasha. Duk da cewa mun fuskanci matsaloli kamar rashin wadataccen mai da kuma tsaiwatar lokacin ruwan sama wadanda suka rage mana kudin shiga da kuma riba a Najeriya, amma duk da haka mun samu riba, sannan hakan ya ba mu kwarin gwiwa komai zai daidaita a gaba.”
Kamfanin Simintin dangote ya samu ribar Naira miliyan 392, inda a shekarar 2013 ya samun ribar 386.