Kamfanin StarTimes ya rage farashi
Masu amfani da manhajar StarTimes sun fara cin moriyar ragin da kamfanin ya yi a farashinsa na talabijin wanda ya fara aiki tun ranar 1 ga watan Satumba. Kamfanin ya sanar da cewa zai rage farashin kallonsa a tsarin Classic daga Naira 2,600 zuwa Naira 1,900, tare da kara wasu tashoshi da ba su a […]
Masu amfani da manhajar StarTimes sun fara cin moriyar ragin da kamfanin ya yi a farashinsa na talabijin wanda ya fara aiki tun ranar 1 ga watan Satumba.
Kamfanin ya sanar da cewa zai rage farashin kallonsa a tsarin Classic daga Naira 2,600 zuwa Naira 1,900, tare da kara wasu tashoshi da ba su a cikin tsarin kamar su EbonyLife Tb da Fod da ST Kids da sauransu.
Kamfanin ya ce ya dauki matakin rage farashin ne domin fadada kasuwancinsu ta yadda wadansu mutane da ba su iya shiga tsarin damar shiga.
Kamfanin na StarTimes ya ce zai ci gaba da nishadantar da masu kallo da shirye-shirye masu kayatarwa da nishadantarwa kamar wasanni da wakoki da wasannin kwaikwayo da fina-finai da sauransu.
Kamfanin ya ce rage farashin zai taimaka wajen fadada kasuwancinsa a Najeriya da kuma tabbatar da cewa mutanen kasar nan sun samu abin da suke so.
Kafin nan, kamfanin na StarTimes ya bayar da sanarwar cewa za a mori tashohinsu kyauta na wata daya a watan Agusta, inda duk mai StarTimes ya kalli kowace tasha.
StarTimes ne kamfanin talabijin mafi girma a yankin Afirka, inda kusan mutum miliyan 20 suke amfani da shi.