Kamfanin sukari na Dangote ya samu ribar N4.6bn a wata 3

Hakan ya nuna an samu karuwar kashi 58 daga Naira biliyan 2.9 a daidai wannan lokacin a bara

Kamfanin sukari na Dangote ya samu ribar N4.6bn a wata 3

Aliko Dangote

Kamfanin yin sukari na dangote ya fitar da rahoton samun ribar Naira biliyan 4.6 a wata uku, wanda hakan ya nuna an samu karuwar kashi 58 daga Naira biliyan 2.9 a daidai wannan lokacin a bara.

Rahoton kudi na kamfanin ya nuna cewa ribar da aka samu tana da nasaba da karuwar kudaden shiga da aka samu na tsawon lokaci, duk da hauhawar farashin kayayyaki.

Kudaden shiga na wannan lokacin ya karu da kashi 62 daga Naira biliyan 64 da aka samu a karshen bara, wanda ya haura zuwa Naira biliyan 103 a cikin wannan shekara ta 2022, sakamakon karuwar kudaden shiga da aka samu daga sayar da sukari.

Jimlar kudaden shiga da aka samu daga abokin ciniki a cikin wata na uku na karshen wannan shekara 2022 shi ne Naira biliyan 14.4, kuma kudaden shiga da aka samun yafi yawa daga abokan huldar kamfanin daga Jihar Legas.

Har ila yau, an samu karin ciniki sosai, inda aka samu kari daga Naira biliyan 55 a bara zuwa Naira biliyan 84 a bana.

Sauran kudaden shigar da kamfanin ya samu sun kai Naira miliyan 61 a cikin wata 3 na wannan shekara ta 2022, idan an kwatanta da wata 3 na warshen shekarar bara da aka samu Naira miliyan 34.

Sai dai kudaden sayar da kayayyaki da rarrabawa, da kuma kudaden gudanarwa, sun ragu zuwa Naira miliyan 188 da kuma Naira biliyan 2.7 daga Naira miliyan 250 da kuma Naira biliyan 2.8, karkashin harkokin yin tafiye-tafiye, tarurruka da dai sauransu.

Jimillar kadarorin kamfanin ta kara habaka daga Naira biliyan 323 a bara zuwa Naira biliyan 474 a bana.