Kamfanin Sukarin Dangote Ya Yi Asarar Biliyan N108.9 A 2023
Kamfanin Sukarin Dangote ya yi asarar Naira biliyan 172.198 a sakamakon musayar kuɗin Najeriya
Kamfanin samar da sukari na Dangote ya bayyana cewa ya yi asarar Naira Biiliyan 108.92 a shekarar da ta gabata.
Kamfanin ya danganta asarar da ya tafka da faduwar darajar Naira, wanda akasari yake sa ribar da kamfanoni suke samu ta zirare.
Kundin bayanan abin da ya faru da shi a 2023, ya bayyana cewa, kamfanin ya yi asarar Naira biliyan 172.198 a sakamakon musayar kuɗin Najeriya da na kasashen waje.
Asarar ta haddasa raguwar kudaden masu zuba jari daga Naira biliyan 171.2 zuwa Naira biliyan 79.2.
- Yunwa: Jama’a sun daka wa motar Dangote wawa a Katsina
- Ba Dangote ne kadai ke shigo da siminti da sukari da gishiri Najeriya ba
Duk da haka raohoton ya nuna cewa a shekarar, kamfanin ya samu karin shigar kudade zuwa Naira Biliyan 441.453 daga Naira Biliyan 403.246 da ya samu shekarar 2022.
Sai dai a zahiri kuma, ribar da aka samu ta ragu zuwa Naira biliyan 86.304 daga Naira Biliyan 91.963 a shekarar 2022, duk da cewa kudin da aka samu ya ƙaru, amma ribar ta zurare.
Dunkulalliyar ribar da kamfanin ya samu kafin ya cire kudin haraji ta ragu zuwa Naira biliyan 76.68 idan aka kwatanta da Naira biliyan 82.41 da aka samu a shekarar 2022.
Kamfanin ya yi asara bayan cire haraji har ta Naira biliyan 73.760 a yayin da ya yi asarar Naira biliyan 54.742 a 2022.
Rigar masu zuba jari a kamfanin kuma ya yi kasa da -N6.07 akan kowane hannun jari idan an kwatanta da N4.51 da suka samu a 2022.