Kamfanin Takin Dangote zai fara aiki a Afrilun bana

Matatar mai kuma a rubu’in farko na badi Babban Bankin Najeriya ya tabbatar da cewa zai tallafa wa shirin Dangote na gina Kamfanin Taki da matatar mai na kimanin Dala biliyan 11. Bankin CBN zai tallafa wa Dangote ne da Naira biliyan 125 domin fara kamfanin takin da zai rika fitar da tan miliyan uku […]

Kamfanin Takin Dangote zai fara aiki a Afrilun bana

Alhaji Aliko Dangote

  • Matatar mai kuma a rubu’in farko na badi

Babban Bankin Najeriya ya tabbatar da cewa zai tallafa wa shirin Dangote na gina Kamfanin Taki da matatar mai na kimanin Dala biliyan 11.

Bankin CBN zai tallafa wa Dangote ne da Naira biliyan 125 domin fara kamfanin takin da zai rika fitar da tan miliyan uku wanda zai fara aiki a watan Afrilun bana.

Da yake jawabi a ziyarar gani-da-ido na tsawon awa hudu a matatar man ta Dangote wadda za ta rika fitar da gangar mai dubu 650, a rana a Jihar Legas, Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emifiele ya ce bankin ya tallafa wa matatar man da Naira biliyan 75, shi kuma Kamfanin Takin da Naira biliyan 50 a karkashin shirin gwamnati na inganta wasu bangarorin tattalin arzikin kasar.

Dangote ne ya dauki nauyin kashi 60 tare da tallafin kashi 40 daga bankunan cikin gida da na waje, sannan Babban Bankin shi ma ya shigo da tallafin Naira biliyan 75 ga matatar mai, da kuma Naira biliyan 50 ga Kamfanin Takin.

“Wannan wani aiki ne da zai ci Dala biliyan 9, wanda kuma bankuna daga nan gida Najeriya da wajen Najeriya suke tallafawa. Shi ma Bankin CBN ya tallafa da Naira biliyan 75 domin matatar man da kuma Naira biliyan 50 domin Kamfanin Takin, wanda ba wani abu ba ne idan aka kwatanta da kudin da za a kashe a ayyukan. Amma za mu ci gaba da tallafa wa mutane ko kamfanonin da suke da niyyar tallafa wa gwamnati da kuma Babban Bankin wajen habaka kasar nan,” inji shi.

Ya ce duk da cewa taki ya kusan wadata a Najeriya yanzu, wannan sabon kamfanin zai kai biyun kamfanin taki na Eleme Petrochemical, sannan ya nanata cewa a lokacin da matatar man ta fara aiki a rubu’in farko na badi, Najeriya za ta wadatar da kanta har ma ta shiga cikin kasashe masu fitar da mai. Sannan ya ce a lokacin da kamfanonin biyu suka fara aiki, Babban Bankin ne zai fara rokon Dangote ya sayar musu da canjin kudaden kasashen waje.

Da yake jawabin godiya kan tallafin Babban Bankin, Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya ce kamfanin na bukatar shawara da goyon bayan bankin domin ci gaba da ayyukan da yake yi.

Sannan ya yi kira ga mutanen Najeriya su ci gaba da ba gwamnati goyon baya wajen habaka tattalin arzikin kasar nan da take yi.

Ya ce “Ina da yakinin wadannan ayyukan za su habaka tattalin arzikin Najeriya, sannan muna addu’ar za mu samu wadansu ’yan Najeriya da za su shigo domin habaka tattalin arzkin kasar nan. Ba wai batun magana ba ce kawai, maganar aiki ne. Dole su sanya dukiyoyinsu ba tare da tsoro ba wajen yin abubuwan da za su taimaka. Da taimakon gwamnati, za mu yi kokarin mun gyara wasu bangarorin kamar yadda muka yi a siminti.”

“A yanzu haka sama da mutum dubu 26 ne suke aiki a wajen ginin kamfanin, sannan kuma idan aka kammala, za a dauki akalla mutum dubu 80, aiki sannan kusan mutum  dubu 50, za su kasance a cikin ginin,” inji   Dangote.