Kamfanin Tecno ya fito da sabuwar waya
Kamfanin da yake kera wayar salula samfurin Tecno ya sake fito da wata sabuwar fasaha inda ya kera sabuwar waya mai suna Boom-J7 wacce ake yi wa lakabi da akwatin kide-kide da raye-raye. Sabuwar wayar salular ita ce ta farko a wayoyin da kamfanin yake son fitowa da su kafin shekarar da muke ciki ta […]
Kamfanin da yake kera wayar salula samfurin Tecno ya sake fito da wata sabuwar fasaha inda ya kera sabuwar waya mai suna Boom-J7 wacce ake yi wa lakabi da akwatin kide-kide da raye-raye.
Sabuwar wayar salular ita ce ta farko a wayoyin da kamfanin yake son fitowa da su kafin shekarar da muke ciki ta kare.
A yayin da kamfanin yake kaddamar da wayar ga dimbin jama’a da suka taru don kashe kwarkwatar idonsu a Jihar Legas, Daraktan kasuwanci na kamfanin, bane Ni, ya ce kamfanin ya kera wayar ne don ya biya bukatun ’yan Najeriya da suke sha’awar kide-kide da raye-raye.
Ya ce ’Yan Najeriya suna mutukar kaunar wakoki da kide-kide da raye-raye, musamman wadanda suke tsakanin shekara 15 da shekar 35 a duniya.
Ya bayyana cewa abu ne a fili cewa ’yan Najeriya suna mutukar son wake-wake da kide-kide amma kuma ba su samu damar samun kafar da za su cin ma burinsu ba.
“Saboda haka dole a yi amfani da hayoyin zamani don bunkasa hajar da za ta samar da wakoki da kide-kide ga manyan gobe masu tasowa ta hanyar wayar salula,” nji shi.
Ya kara da cewa sabuwar waya ce ta zamani wacce ta kunshi duk wata manhaja da wayoyin zamani suke da shi.
Sai dai kuma ya ba da tabbacin cewa sabuwar wayar tana da manhajar daidaita sauti na musamman.