Kamfanoni 700 na neman kwangilar aikin jirgin kasa
Akalla kamfanoni 700 ne ke neman kwangilolin da Hukumar Jiragen Kasa ta Najeriya (NRC) za ta bayar a 2020. Ayyukan sun shafi sayo kaya da zartar da ayyuka da kuma lura da su, wadanda NRC ta ce za ta tabbatar da bin ka’ida wajen yin su. “Mun bullo da hanyoyin cikin gida na tabbatar da […]
Akalla kamfanoni 700 ne ke neman kwangilolin da Hukumar Jiragen Kasa ta Najeriya (NRC) za ta bayar a 2020.
Ayyukan sun shafi sayo kaya da zartar da ayyuka da kuma lura da su, wadanda NRC ta ce za ta tabbatar da bin ka’ida wajen yin su.
“Mun bullo da hanyoyin cikin gida na tabbatar da kammala matakin tare da kokarin ganin an yi komai a fili bisa doka”, inji NRC.
Shugaban hukumar, Fidet Okhiria ya ce za a hanzarta kammala ayyukan kasancewar COVID-19 ta kawo tsaiko.
Saboda COVID-19 kamfanonin ba su je wurin taron ba, said dai ta bidiyo suka hallara, domin kauce wa cunkoso.
Masu sa ido da kungiyoyin kare hakki da kungiyar injiniyoyi ta Naejriya (NSE), sun hallara domin ganin yadda tsarin ya gudana.
“Masu neman kwangilar ba sa nan, amma duk da haka za mu tabbatar an bi ka’idojin gwamnati.
“Shi ya sa muka gayyato masu sa ido su wakilce su wurin shaida abin da ya faru.
Okhiria ya yi wa taron jawabi ne ta bakin Darektar Ayyukan hukumar, Misis Niyi Alli.
Darektan Sayayya, Ben Iloanusi ya ce “Akwai kwangiloli uku na sayen kaya, tara na aiwatar ayyuka da kuma biyar na lura da kwarewa”.