Kamfanonin cakulan sun dumfari dazukan Kodebowa

Manyan kamfanonin alawar cakulan na duniya da suka hada da Mars da Nestle da Mondelez a kokarinsu na neman kokon da za su sarrafa a masana’antunsu, sun dumfari dazukan Kodebowa, inda suke sare itatuwa da wuraren shakatawa da suka shahara a wannan kasa da ke Afirka ta Yamma. Wadannan kamfanoni tuni suka sassake wannan hamshakin […]

Kamfanonin cakulan sun dumfari dazukan Kodebowa

Manyan kamfanonin alawar cakulan na duniya da suka hada da Mars da Nestle da Mondelez a kokarinsu na neman kokon da za su sarrafa a masana’antunsu, sun dumfari dazukan Kodebowa, inda suke sare itatuwa da wuraren shakatawa da suka shahara a wannan kasa da ke Afirka ta Yamma.

Wadannan kamfanoni tuni suka sassake wannan hamshakin dajin kasar da ya shahara da itatuwa, inda a halin yanzu kashi 80 cikin 100 na daji da a shekarar 1960 ke cike da itatuwa yanzu babu shi.

Kimanin kashi 40 cikin 100 na kokon duniya yana samuuwa ne daga kasar Ibory Coast don haka kamfanonin da ke sarrafa alawa samfuran Mars bars da Ferrero Rocher da Milka bars na gudanar da mummunar hada-hadar kasuwancin Cocoa.

Jaridar Giardian ta Birtaniya ta tura wakili zuwa Kodebowa, wanda ya bi mata kadin lamarin, har ya tattara bayanai kan yadda aka sare katafaren daji don noman koko (cocoa), har ta kai ga an sare itatuwan da ke tsaye suka kawata wuraren shakatawar al’umma. Su kuw ajami’an hukuma da ke da alhakin kare wadannan muhimman wurare suna karbar rashawa, sai su kawar da ido daga mummunar hada-hadar kasuwanci da ’yan baranda ke yi a kasar.

Da aka tuntubi kamfanonin Mars, Mondelez da Nestle ’yan kasuwar kamfanonin Cargill & Barry Callebaut ba su karyatsa wannan haramtaccen kasuwanci tare da sare itatuwa ba bisa ka’idar da doka ta tanar ba.

Kimanin kashi 70  cikin 100 na koko (cocoa) da ake amfani das hi a fadin duniya a samunsa ne a Afirka ta Yamma, wato kasashen da suka hada da Saliyo da Kamaru, sai dai na Ibory Coast da Ghana su ne mafi kimar daraja da girma, kuma na daya da na biyu a duniya.

Bincike sare dazukan dai ya nuna cewa an samu dama ne saboda talaucin da ya baibaye al’umma, har ta kai ga ba za su iya sayen dunkulen alawar cakulan ba.

Tun a shekarar 2010 kamfanonin suka yi alkawarin hana sare dazuka, inda suka kuduri aniyar shawo kan lamarin nan da shekarar 2020. Barry Parkins jami’in kula dorewar dazuka y ace “sun jajirce wajen shawo kan sare dazukan a hada-0hadar samar da koko. Don haka ma Nestle ta dauki lamarin a matsayin mummunar illata muhalli da ke ci wa duniya tuwo a kwarya.;”

Sai dai babu daya daga cikin kamfanonin da ya ce za su sake farfado da dazukan da suka sare saboda noman koko. Sai dai kokarin gwamnati zai fi tasiri fiye da na kamfanonin, a cewar Richard Scobey na cibiyar hada-hadar koko ta duniya.