Kamfanonin jiragen sama sun koka kan karancin fasinjoji

Hakan na zuwa ne duk da ragin kudin tikiti da kamfanonin suka yi don samun kasuwa.

Kamfanonin jiragen sama sun koka kan karancin fasinjoji

Wasu matafiya a filin jirgin sama

Kamfanonin jiragen sama a Legas sun koka a kan karancin fasinjoji masu tafiye-tafiye zuwa garuruwa daban-daban don yin hutun Sallah duk da kwana uku da Gwamnatin Tarayya ta bayar da hutu don yin bikin a wannan shekarar.

Sun ce babu tururuwar fasinjoji kamar yadda aka saba gani a irin wannan lokaci na bikin Sallah ko makamancinsa.

Wakilinmu ya gano cewa yawancin jiragen saman da ke jigilar fasinjoji daga Legas zuwa wasu jihohi suna fama da karancin fasinjojin.

Hakan na zuwa ne duk da ragin kudin tikiti da kamfanonin suka yi don samun kasuwa musamman a tashar jiragen sama ta Murtala Mohammed da ke Ikeja.

Farashin tikiti daga Legas zuwa Abuja ya koma Naira 85,000 a jirgin Air Peace. Sai kuma Naira 120,000 a jirgin Ibom Air, duka a maimakon Naira 150,000.

Wani jami’in daya daga cikin kamfanonin jiragen saman da wakilinmu ya yi hira da shi, ya bayyana cewa rashin tururuwar jama’ar ba zai rasa nasaba da matsin tattalin arziki ba da kuma sanarwar da gwamnati ta yi na karin hutu a kurarren lokaci.

“Gaskiya lokacin cinkoso da turereniya a irin wannan lokaci ya wuce.

“Domin kamar yadda ka ke gani an samu fasinjoji kashi 80 a wasu jiragen da ke daukar mutane 150 a inda wanda yake daukar mutum 120 a bisa tsari. Wasu kuma an samu fasinjoji 80 zuwa 90,” in ji shi

Wike ya ƙwace filayen jiga-jigan ’yan siyasa a Abuja

Gwamnoni sun ƙi amincewa da ƙara harajin VAT

Matashi ya kashe mahaifinsa kan N5,000 a Delta

Muhimman batutuwa da Biden ya taɓo a jawabin yi wa Amurkawa bankwana