Kamfanonin sadarwa na neman ƙara kuɗin kira da na data

Kamfanonin sadarwar sun ce su kaɗai ne ba su yi ƙarin farashi ba wanda ke barazana ga ɗorewar kamfanonin.

Kamfanonin sadarwa na neman ƙara kuɗin kira da na data

Manyan kamfanonin sadarwar (Glo, MTN, Airtel da 9Mobile) a Najeriya na neman sahalewar gwamnati domin su ƙara kuɗin kira da na data.

Kamfanonin sadarwar sun bukaci ga gwamnatin da sakar musu mara ta kuma ba su damar gabatar da batun ƙarin kudin ta hanyar tattaunawa da masu ruwa da tsaki.

A cewarsu, tsarin ƙayyade musu farashin kuɗin kira da na data na yanzu bai dace da yanayin tattalin arziki ba, don haka suke neman taimakon gwamnati don magance ƙalubalen da suke fuskanta.

Kamfanonin sadarwan guda huɗu sun ce su kaɗai ne ba su sauya farashinsu ba, wanda kuma hakan barazana ce ga ɗorewarsu da kuma yiyuwar rage ƙwarin gwiwar masu zuba jari.

Sun bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar haɗin gwiwa da ƙungiyar kamfanonin sadarwa ta Najeriya (ALTON) da Ƙungiyar kamfanonin sadarwa ta Najeriya (ATCON) suka fitar a ranar Alhamis.

A cewar sanarwar mai ɗauke da sa hannun shugaban ALTON, Mista Gbenga Adebayo, da shugaban ATCON, Mista Tony Emokpere, ba a yi wa tsarin farashin gyara na gaba ɗaya ba a cikin shekaru 11 da suka gabata.

Sun danganta rashin ƙaruwar farashin ga matsalolin da suka shafi dokar ƙayyade musu farashi, duk da matsalar tattalin arziki da ake fuskanta

Sun ce: “Tsarin kula da farashi na yanzu, bai dace da yanayin tattalin arziki ba, kuma yana barazana ga ɗorewar kamfanonin kuma yana iya lalata amincin masu zuba jari.

“Duk da taɓarɓarewar tattalin arziki, kamfanonin sadarwa sun kasance masana’anta ɗaya tilo da har yanzu ba ta sake nazarin tsarin farashin ayyukansu ba a cikin shekaru 11 da suka gabata, musamman saboda takunkumin gudanar da tsare-tsare da aka sa musu.

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta