Kamfanonin waya sun rasa masu amfani da Intanet dubu 100 a Agusta – Rahoton NCC
A karo na biyu a bana, dubban ’yan Najeriya sun rage u amfani da layukansu wajen shiga Intanet a watan Agusta. Kamar yadda rahoton Hukumar NCC ya bayyana, inda ya ce masu amfani da Intanet mutum miliyan 122 da dubu 585 da 515, maimakon miliyan 122 da dubu 681 da 418 a watan Yuli. A […]
A karo na biyu a bana, dubban ’yan Najeriya sun rage u amfani da layukansu wajen shiga Intanet a watan Agusta.
Kamar yadda rahoton Hukumar NCC ya bayyana, inda ya ce masu amfani da Intanet mutum miliyan 122 da dubu 585 da 515, maimakon miliyan 122 da dubu 681 da 418 a watan Yuli.
A watan Janairun bana sun ragu da mutum dubu 33,233.
Rahoton ya nuna cewa MTN ya rasa mafi yawan masu amfani da Intanet din, masu amfani da Intanet a layin MTN sun kai miliyan 51 da dubu 602 da 25, inda suka ragu da dubu 600,000 idan aka kwatanta da miliyan 52 da dubu 269 da 270 a watan Yuli. MTN na ci gaba da zama wanda aka amfani da layinsa wajen shiga Intanet.
Airtel ne ya zo na biyu da mutum miliyan 32 da dubu 753 da 406. Sai Globacom mai miliyan 29 da dubu 521 da 597. Kamfanin 9mobile ya ci gaba da asarar masu amfani da layinsa wajen shiga Intanet, yana da mutum miliyan 8 da dubu 625 da 5 a Agusta.
A daidai lokacin da tsarin wayar salula na (BoIP) yake kara samun karbuwa, ya samu karin masu shiga tsarin da mutum 3,000 a watan Agusta, inda yanzu suka kai 380.274.
A cikin layukan waya masu amfani guda miliyan 176,897,879 a Najeriya kamar yadda kididdigar watan Agusta ta nuna, MTN ke kan gaba da mutum 65,707,899 wato kashi 37. 20. Sai Airtel ke biye da miliyan 47,921,891 wato kashi 27.13 sai Globacom da miliyan 47,265,628 wato 26.7.
Sai 9mobile mai miliyan 15,602,255 wato kashi 9. Sabon Kamfanin Bisafone ya samu kashi 0.07 wato mutum 119,386.
Duk da sun rasa kimanin miliyan hudu masu amfani da yanar gizo daga Janairun shekarar 2017, amma 9mobile ya ci gaba da samar da sadarwa mafi inganci a Najeriya kamar yadda kididdiga ta nuna.
An samu karin masu amfani da wayoyin salulu, inda NCC ta ce an samu karin sababbin masu amfani da waya su 7,316 wato kashi 70 a watan Agusta.
Globacom bai samu karin da yawa ba, inda ya samu karin 575, Airtel da MTN suka samu 1,435 da 1,714.
Da karin da aka samu na masu amfani da layuka, Hukumar Sadarwa ta samar wa kasa kudin shiga. Wanda ya nuna an samar da karin kashi 10.11a farkon shekara. Acikin wannan tsarin kuma, ta samar wa kasa da abin da za a ga kokarin hukuma wajen cigaban tattalin arziki.