Kamfanonin wutar lantarki sun sami lamunin Naira biliyan 158 don biyan bashi

Sababbin wadanda suka mallaki rushashshen kamfanin wutar lantarki  na PHCN sun samu lamunin Naira biliyan 158 daga babban bankin Najeriya na CBN karkashin shirin cibiyar daidaita kasuwancin wutar lantarki NEMSF.   Shirin wanda da farko ya tanadi kimanin Naira biliyan 213 an tsara shi ne tun watan Satumban shekarar 2014 don biyan bashin da kamfanonin […]

Kamfanonin wutar lantarki sun sami lamunin Naira biliyan 158 don biyan bashi

Sababbin wadanda suka mallaki rushashshen kamfanin wutar lantarki  na PHCN sun samu lamunin Naira biliyan 158 daga babban bankin Najeriya na CBN karkashin shirin cibiyar daidaita kasuwancin wutar lantarki NEMSF.
 
Shirin wanda da farko ya tanadi kimanin Naira biliyan 213 an tsara shi ne tun watan Satumban shekarar 2014 don biyan bashin da kamfanonin da suka gaji kamfanin wutar lantarki na PHCN suka gada a ranar daya ga watan Nuwamban shekarar 2013.
 
To amma har yanzu ba a bayar da kimanin naira biliyan 51 da digo takwas ga kamfanoni 40 da suke cikin tsarin ba.
 
Sai dai Bankin CBN ya ce ya bayar da Naira biliyan 158 da digo bakwai ga kamfanonin 37 tun shekarar 2015.


A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya