Kammala zabe gobe a jihohi biyar
A ranar Talatar makon jiya shekaranjiya ne Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ce ba ta kammala zabe a wasu jihohi biyar zuwa shida na kasar nan ba, don haka ta sanya gobe Asabar ta zama ranar da za ta gudanar da karashin zaben a wasu mazabu na jihohin da niyyar tantance […]
A ranar Talatar makon jiya shekaranjiya ne Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ce ba ta kammala zabe a wasu jihohi biyar zuwa shida na kasar nan ba, don haka ta sanya gobe Asabar ta zama ranar da za ta gudanar da karashin zaben a wasu mazabu na jihohin da niyyar tantance Gwamnan da zai samu nasara. Jihohin da za a kammala zabubbukan a gobe su ne na Sakkwato da Binuwai da Kano da Adamawa da Filato.
Jiha ta shida da ake tababar yin zaben a cikinta ita ce ta Bauchi, wadda a bayan nan Hukumar INEC, ta aminci a sa sakamakon zaben Karamar Hukumar Tafawa Balewa, wanda a baya Babban Jami’in Tattara Sakamakon Zaben Gwamnan Jihar ya ki karbarsa bisa ga korafin da Baturiyar zaben Karamar Hukumar, Uwargida Diminion Anosike ta yi cewa akwai hargitsi da yamutsi da ta da husuma, har ma da cin zarafi da suka wakana a lokacin zaben na ranar 9 ga Maris. Sannan Hukumar ta INEC ta fadi cewa zuwa yanzu ta rage kuri’un Karamar Hukumar Ningi a Jihar Bauchi daga 25,000, zuwa 2,500.
Matsayin da Jam’iyyar APC, mai mulki a jihar ta sa kafa ta shure, yayin da Jam’iyyar adawa ta PDP, ta ce tana maraba da shi. Makomar zaben Gwamnan Jihar Ribas ma ana can ana cece-kuce a kanta tsakanin Hukumar INEC da Jam’iyyar APC. Zargin an tayar da hayaniya da yamutsi da kuntata wa Turawan zabe da ma masu kada kuri’a, su suka haddasa aka kasa kammala zabubbukan a wadancan jihohi da na ambata. Akwai kuma zargin rashin isar kayayyakin zabe da Turawan zabe a tashoshi a kan lokaci da gazawar na’urar tantance masu kada kuri’a da aka ce ya taka muhimmiyar rawa cikin ka sa kammala zabubbukan a kan lokaci, a zaben gwamnonin da na ’yan Majalisar Dokokin Jihohi da aka gabatar a duk fadin kasar nan ranar 23 ga Maris din.
Rashin yarda da kaddarar nasara ko faduwa zabe ta ’yan siyasar kasar nan ta sanya ake ta wadannan cece-kuce da zargin juna da ita kanta Hukumar INEC, tsakanin ’ya’yan Jam’iyyar APC da na PDP, ta yadda kowa na zargin kowa a inda bai yi nasara ba. Misali, Shugaban Jam’iyyar PDP na Kasa, Mista Uche Secondus ya yi zargin cewa sakamakon zaben jihohi hudu daga cikin wadancan jihohi shida da aka ce zabubbukansu ba su kammala ba, jam’iyyarsa ce take kan gaba. A Jihar Bauchi ma Shugaban Jam’iyyar APC reshen jihar Alhaji Uba Nana shi ya sa kafa ya shure matsayin da Hukumar INEC ta dauka a baya-bayan nan na amincewa da zaben Karamar Hukumar Tafawa Balewa.
Tanade-tanaden sassa na 26 da na 53, na Dokar Zabe ta shekarar 2010, da aka yi wa kwaskwarima, su suka tanadi cewa muddin jimmilar kuri’un da aka yi wa rijistar yin zabe a yankin da aka kasa yin zabe ko aka soke zabe, suka zarta yawan da aka samu tsakanin dan takarar da ya zo na daya da na biyu a cikin zabe, dole a sake zabe a wuraren. Ma’ana muddin kuri’un da aka soke, za su iya canja sakamakon zabe, to, kuwa zabe bai kammala ba, bare a ce ga wanda ya yi nasara, kamar yadda wadannan sassa suka fayyace.
Mai yiwuwa kasancewa a wannan zaben shi jama’ar kasa suka fara ganin aikin fassarar wadancan sassa biyu da har a zabubbuka 23, Hukumar ta INEC ta bayyana ba a kammala zabubbukansu ba. Kodayake a zaben 2011, an samu 2, a shekarar 2013, an sake samun 2, sai a shekarar 2015 da aka samu 4, na 2018, da aka samu 1, wato na zaben Gwamnan Jihar Ekiti.
Bayan zaman zullumi da kusan dukan ’yan kasa suke ciki musamman mutanen da ke jihohin da za a kammala zabubbukan a gobe. Akwai kuma zarge-zarge masu karfin gaske da ake yi wa ’yan siyasar wadancan jihohi musamman na jam’iyyun APC da PDP, cewa kowannensu yana ta shirya magudi iri-iri kama daga saye kuri’un masu zabe tun yanzu da sauran tanade-tanaden da suke ganin za su kai su ga nasara, tare da kiraye-kiraye ga Hukumar INEC da lallai ta tabbatar ta gudanar da kammala zabubbukan cikin kamanta gaskiya da adalci.
Masu iya magana dai kan ce ruwan da ya buge ka shi ne ruwa, Ni a Kano nake da zama, jihar da take kan gaba a kan dukan jihohin Arewa a cikin wasu muhimman al’amuran yau da kullum, musamman kasuwanci da siyasa, jihar da tun a Jamhuriya ta Farko tauraruwar siyasarta take haskawa (ba wai lallai ba ne a ce a kullum alheri take haskawa). Zaben Kano na gobe za a kammala shi ne tsakanin dan takarar Jam’iyyar PDP da na APC wato Injiniya Abba Kabir Yusuf da ya samu kuri’u 1,014,474 da Gwamnan Jihar mai ci, Dokta Abdullahi Umar Ganduje da ya samu kuri’a dubu 987 da 819, wato Injiniya Abba Kabir ya ba Gwamna Ganduje ratar kuri’a dubu 26 da 655.
Dukan wadannan ’yan takara biyu, mai karatu ka sani tushensu daya na siyasa tun daga fara wannan Jamhuriya ta Hudu, wato tun daga 1999, har zuwa shekarar 2015 a karkashin tafiyar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso suke yi ko a cikin gwamnati ko bayan barinta. Karewa da karau Gwamna Ganduje shi ya gaji Sanata Kwankwaso a zaman Gwamnan Jihar Kano a shekarar 2015, bayan sun zauna da shi a zaman mataimakinsa har karo biyu 1999 zuwa 2003, da kuma 2011 zuwa 2015. Yayin da Injiniya Abba ya kasance Kwamishina da kuma mataimaki na musamman ga Sanata Kwankwaso. Ba ma wannan ba maganar da ake yi Injiniya Abba ’yar dan uwan Sanata Kwankwaso yake aure. Na kawo dan wannan tarihi ne don mai karatu ya kara fahimtar yadda dambarwar take, amma dai a wannan zabe an rabu haihata-haihata, ba a ga maciji da juna, sai ko nan gaba wata bukatar siyasar ta sake hada su.
A mazabu 172 da suke da masu kada kuri’a dubu 128 da 572 da ke kananan hukumomi 30, daga cikin 44 da ke jihar ne Hukumar INEC ta ce ba a kammala zaben ba, kuma a cikinsu za ta sake zaben a gobe in Allah Ya kai rai, a Jihar Kano. Idan ka debe kananan hukumomin Dala da ta cikin Birni da Kewaye da Nasarawa, sauran kananan hukumomin 27, suna wajen birnin Kano ne, wato suna karkarar jihar. Sakamakon zaben Gwamnan da yanzu ake ja-in-ja a kansa ya nuna cewa dan takarar Jam’iyyar PDP, Alhaji Abba kasancewarsa dan cikin birni ya fi samun kuri’unsa daga kananan hukumomin birnin Kano da kewaye, yayin da Gwamna Ganduje da ya fito daga karkara, ya fi samun kuri’unsa daga kananan hukumomin karkara. Ko a haka za a kwatanta?
Sanin yanayin siyasar Jihar Kano ne ya sanya tuntuni Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Muahammadu Sanusi II, yake ta jagorancin addu’o’i da yin jawabai ga al’ummar jihar a kan a yi zabe lami lafiya. Ita ma Kungiyar Dattawan Jihar Kano a karkashin jagorancin Alhaji Bashir Othman Tofa a taron manema labarai da ta yi a wannan mako, bayan rokon jama’a da ta yi a kan a yi zabe lami lafiya, ta kuma nemi a bar jama’ar jihar su zabi abin da su ke so. Mu ma daga nan muna addu’ar Allah Ya sa a yi dukan wadannan zabubbuka a ko’ina lami lafiya, amin.