Kamun kai ga rayuwar Kirista

Ya fi kyau ka zama mai hakuri da ka zama mai karfi. Ya fi kyau ka iya mallakar kanka fiye da mallakar birane.”(Karin Magana 16:32) Godiya ta tabbata ga Allah Ubangiji domin yawan kaunarSa zuwa gare mu. A wannan mako za mu yi nazari ne a kan yadda mai bin Yesu Almasihu ya kamata ya […]

Kamun kai ga rayuwar Kirista
Kamun kai ga rayuwar Kirista

Ya fi kyau ka zama mai hakuri da ka zama mai karfi. Ya fi kyau ka iya mallakar kanka fiye da mallakar birane.”(Karin Magana 16:32)

Godiya ta tabbata ga Allah Ubangiji domin yawan kaunarSa zuwa gare mu. A wannan mako za mu yi nazari ne a kan yadda mai bin Yesu Almasihu ya kamata ya zama, wato ta bangaren kamun-kai. Za mu iya  cewa kamun-kai a cikin rayuwar mai bin Yesu Almasihu shi ne iya guje wa yin zunubi ta wurin kiyaye tafarkin Ubangiji Allah. Kolosiyawa 3:5-10: “Saboda haka, sai ku kashe zukatanku ga sha’awace-sha’wacen duniya, wato fasikanci da aikin lalata da muguwar sha’awa da mummunan buri, da kuma kwadayi, wanda shi ma bautar gumaka ne. Saboda wadannan abubuwa ne fushin Allah yake sauka a kan kangararru. A da kuna bin wadannan sa’ad da suke jiki a gare ku. Amma yanzu sai ku yar da duk wadannan ma, wato fushi da hasala da keta da yanke da alfasha. Kada ku yi wa juna karya da yake kun yar da halinku na da da ayyukansa, kun dauki sabon halin nan da ake sabuntawa ga sani, bisa ga kamannin Mahaliccinsa. Duk mai bin tafarkin Ubangiji sabon halitta ne cikin Yesu Almasihu. (2 Korintiyawa 5:17). Tsohon al’amari duk zai shude, Ubangiji zai maye gurbin da albarkar ruhunSa, lallai idan kana dauke da albarkarSa, ba za ka taba zama da sha’awar yin karya, kishi, lalata, gulma, kwadayi, kisa da makamantansu ba, jama’a kuma za su shaida cewa lallai wannan mutum mai kamun-kai ne mai tsoron Allah kuma, Ubangiji kuwa zai sa maka albarkunSa mara kimantuwa.

Rashin kamun-kai na kai mutum ga hallaka, yau za ka gan shi (mara kamun-kai) nan yana kaiwa da kawowa, kwadayi shi ne, karya bai bari ba, gulmace-gulmace shi ne a gaba, idan ka ji ana fada za ka tarar da shi nan, kisa yana wajen, kwadayi shi ne mai jagora… ai ba sai wani ya fada maka cewa irin wannan mutum ba ya da kamun-kai ko ba ya dauke da albarkar ruhu ba, halinsa kadai shaida ne a kansa. Shi ya sa yana da muhimmanci mu yi rayuwarmu bisa ga tafarkin Allah wanda yake dauke da albarkar ruhu domin halinmu na mutuntaka yakan kai mu ga hallaka, Romawa 8:13: “In kuna zaman halin mutuntaka, za ku mutu ke nan, amma in da ikon Ruhu kuka kashe ayyukan nan na halin mutuntaka, sai ku rayu.”

Idan muka yi bincike cikin Littafi Mai tsarki za mu ga misallai da dama da rashin kamun-kai ke haifarwa, misali:

  1. Karya doka (Farawa 3:16-18)

“Ga matar kuwa ya ce, “Zan tsananta nakudarki ainun da azaba za ki haifi ’ya’ya, duk da haka muradinki zai koma ga mijinki, zai kuwa mallake ki. Ga Adamu kuwa ya ce, Ka kasa kunne ga muryar matarka, har ka ci daga ’ya’yan itacen da na dokace ka, ‘Kada ka ci daga cikinsu.’ Tunda ka aikata wannan za a la’antar da kasa saboda kai da wahala za ka ci daga cikinta muddin rayuwarka. Ƙayayuwa da sarkakkiya za ta ba ka, za ka kuwa ci ganyayen saurar. 19. Za ka yi zufa da aiki tukuru kafin ka samu abinci, har ka koma kasa, gama da ita aka siffa ta ka, kai turbaya ne, ga turbaya kuma za ka koma.”

  1. Kishi da kisa (Farawa 4)
  2. Hanzarin biyan bukatar jiki (yunwa) (Farawa 25:27-34)
  3. Kwadayin kayan duniya (Farawa 19:15-26)
  4. Fushi (Fitowa 2:14) da dai makamantansu.

Hakan nan kuma misalin wadanda suka nuna halin kamun-kai,

Kamar:

  1. Yusufu da Matar Fotifar (Farawa 39)
  2. Dawuda Ya Bar Saul da Rai a En-gedi (1 Samaila 24,26)
  3. Rayuwar Yesu Almasihu (Matiyu 4:1-11, Ibraniyawa 4:15).

Abin nazari:

Yakubu 1:19-20 “Ya ’yan uwana kaunatattu! Ku san wannan, wato, kowa ya yi hanzarin kasa kunne da jinkirin yin magana, da kuma jinkirin yin fushi, don fushin mutum ba ya aikata adalci. Saboda haka, sai ku yar da kowane irin aikin kazanta da keta iri-iri, maganar nan da aka dasa a zuciyarku, ku yi na’am da ita a cikin halin tawali’u, domin ita ce mai ikon ceton rayukanku.”

A zaman mai bin Yesu Almasihu ya kamata ya zama yana dauke da kauna, kaunar Ubangiji da dukkan zuciyarka da dukkan ranka da kuma dukkan hankalinka, sa’anan ka kaunaci dan uwanka kamar kanka. (Matiyu 22:37). Idan kuwa muka iya yin wannan, kamun-kai zai bayyanna cikin kowane hali da muka samu kanmu, domin idan kana dauke da kaunar Allah a cikin zuciyarka kana kuma kaunar dan uwanka, ba za ka ci amanar makwabcinka ba, ba za ka yi gulmarsa ga wani ba, ba za ka zama mai saurin fushi ba, ba kuwa za ka zama mai tada hankalin jama’a ba. Za ka zama mai kama-kanka cikin zamanka da mutane, kana dauke da tsoron Ubangiji a cikin zuciyarka a koyaushe, ba ka kuwa barin zunubi ya mallaki zuciyarka. Romawa 6:12-13: Saboda haka, kada ku yarda zunubi ya mallaki jikin nan naku mai mutuwa har da za ku biye wa muguwar sha’awarsa. Kada kuma ku mika gabobinku su zama kayan aikin mugunta, don yin zunubi. Amma ku mika kanku ga Allah, kamar waɗanda aka raya bayan mutuwa, kuna mika gabobinku ga Allah kayan aikin adalci.

Za mu rufe bincikenmu da 2 Bitrus 1:3-8 “Allah da ikonSa Ya yi mana baiwa da dukan abubuwan da suka wajaba ga rayuwa da kuma binSa, ta sanin wanda ya kira mu ga samun daukakarSa da fiffikonSa, wadanda kuma ta wurinsu ya yi mana baiwa da manyan alkawuranSa masu daukaka kwarai, domin ta wurin wadannan ku zama masu tarayya da Allah a wajen dabi’arsa da yake kun tsira daga bacin nan da ke a duniya da muguwar sha’awa take haifa. Saboda wannan dalili musamman, sai ku yi matukar himma, ku kara ban-gaskiyarku da halin kirki, halin kirki da sanin ya kamata, sanin ya kamata da kamun-kai, kamun-kai da jimiri, jimiri da bin Allah, bin Allah da son ’yan uwa, son ’yan uwa kuma da kauna. In kuwa halayen nan sun zama naku ne, har suna yalwata, za su sa ku kada ku yi zaman banza, ko marasa amfani a wajen sanin Ubangijinmu Yesu Almasihu.

Bari kaunar Allah Uba da zumuntar Ruhu mai starki ya kasance da mu daga yanzu da har abada, amin.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos