Kamun ludayin jagora a kwanaki 100 na Gwamnatin APC

Idan Allah Ya kaimu gobe Asabar gwamnatin tsakiya da jam`iyyar APC  ta kafa a ranar 29 ga watan Mayun da ya gabata, a karkashin shugabanci Alhaji Muhammadu Buhari take cika kwanaki 100 cif-cif, akan karagar mulki, bayan ta yi nasarar karbar mulki daga jam`iyyar PDP, a cikin babban zaben kasar na bana, nasarar da ita […]

Kamun ludayin jagora a kwanaki 100 na Gwamnatin APC
Kamun ludayin jagora a kwanaki 100 na Gwamnatin APC

Idan Allah Ya kaimu gobe Asabar gwamnatin tsakiya da jam`iyyar APC  ta kafa a ranar 29 ga watan Mayun da ya gabata, a karkashin shugabanci Alhaji Muhammadu Buhari take cika kwanaki 100 cif-cif, akan karagar mulki, bayan ta yi nasarar karbar mulki daga jam`iyyar PDP, a cikin babban zaben kasar na bana, nasarar da ita ce ta farko irinta da jam`iyyar adawa ta taba samu, ba wai a wannan mulkin na janhuriya ta hudu ba, da aka fara a shekarar 1999, a `a tun ma daga lokacin da kasar nan ta samu `yancin kai daga Turawan mulkin mallaka na kasar Birtaniya a shekarar 1960.  
 Samun nasarar jam`iyyar ta APC, da take jam`iyyar hadaka daga rusassun jam`iyyun adawa na ANPP da ACN da CPC da wani bangare na APGA, a wancan lokacin da kuma irin yadda `yan kasa musamman talakawa suka dage da addu`o`i da kuma bayar da gudummuwar dari da kwabo dinsu ga dan takarar neman shugabancin kasa na jam`iyyar ta APC Alhaji Muhammadu Buhari, da jajircewar da suka yi wajen fitar farin dango wajen kada kuri`unsu ga dai Buharin, duk a bisa ga imanin da suka yi cewa shi jajirtacce ne, kuma mai amana da zai iya kawo CHANJIN da suke sa rai. Bisa ga yadda kusan komai ya tabarbare, da kuma irin yadda Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, wato INEC, a karon farko ta bullo da tsarin amfani da katin kada kuri`a na din-din-din da na`urar tantance masu kada kuri`ar, sai uwa uba irin matsin lambar da Shugaba Jonathan ya rinka samu, musamman daga kasashen waje irinsu Amurka da na Turai, da suka rinka jan kunnensa akan lallai ya tabbatar da cewa an yi sahihin zabe, wanda duk ya ci a tabbatar da an bashi, wato ma`ana kar ya kuskura ya ce zai murde zabubbukan, wadannan duk suna daga cikin abubuwan da suka yi sanadiyar da Allah SWT Ya kawo  Alhaji Buhari akan karagar mulkin kasar nan.
 A bisa ga tsarin mulkin kasar Amurka da kasar nan take aiki da shi, ya zama al`ada a duk lokacin da aka rantsar da shugaban kasa ko gwamnan jiha akan sabon wa`adi, to, akan saurara musu zuwa kwanaki 100, na farko, wanda a cikin wannan wa`adi shugaban kasa ko gwamnan jiha zai fara yekuwar nasarorin da ya samu a zaman fara cika alkawarin da ya dauka tun a lokacin yakin neman zabe. Tunda haka abin ya ke, bari mu duba wasu daga cikin irin alkawurran da Alhaji Buhari da jam`iyyarsa ta APC suka dauka mu ga ko sun fara cika su ko tukuna.Akwai dai maganar inganta matakan tsaro da samar da ayyukan yi, musamman ga matasa da kuma yaki da cin hanci da rashawa. A `yar fahimtata wadannan a dunkule su za su samar da zaman lafiya kwanciyar hankali da karuwar tattalin arzikin kasa da na mutanenta, rashinsu kamar yadda muka gani a kasar nan su ke haifar da annoba iri-iri ga kasa da jama`arta.
Allah Ya sa ni wannan makala ba za ta iya daukar dukkan ayyukan da gwamnatin tarayya ta Alhaji Muhammadu Buhari ta yi ba a zaman fara cikasa alkawari a cikin wadannan kwanaki 100, duk da ya ke ya dauki kwanaki 100, din bai nadaMinistocinsa ba, (wanda shi ne lokaci mafi tsawo da aka taba samu daga wajen gwamnatin tarayya a cikin tarihin mulkin dimokuradiyyar kasar nan). Don haka wannan ya zama wani babban abin cece-kucen akan gazawar gwamnatin, musamman daga `yan adawa da har suka fara kiraye-kirayen in bai shirya yin mulkin ba ya hamzarta sauka.
 Batu na farko kuma mai matukar muhimmancin gaske, wanda kuma ba ya cikin manyan alkawurran da ta yi, shi ne yadda jihohin nan 27 da wasu Hukumomin ita kanta gwamnatin tarayyar ba su biya albashin ma`aikatunsu ba na wata daya zuwa watanni tara, a zaman ba su da kudin, batun da ya zuwa yanzu jihohin Kwara da Zamfara, tuni sun cikasa ka`idojin da Babban Bankin kasar nan da Shugaba Buhari ya dora wa alhakin nemo hanyoyin da za a warware wannan batu, har sun fara samun bashin kudin da suke bukata, don biyan albashin ma`aikatansu, ya yin da sauran jihohi suna kan hanya.    
 Akwai kuma batun fita zuwa kasashen waje, inda da farko Shugaba Buhari ya amsa gayyatar halartar taron kungiyar kasashen nan bakwai mafi karfin tattalin arzikin masa`antu a duniya da ake wa lakabi da G7, inda a wajen taron nasu suka bashi tabbacin taimaka masa da dukkan abubuwan da ya kabukata da za su kai shi ga nasara. Ya sake amsa gayyatar Shugaban kasar Amurka Mista Barak Obama da wasu daga cikin makarraban gwamnatinsa da manyan `yan kasuwar kasar ta Amurka, wadanda a tattaunawa da Shugaba Buhari a lokuta daban-daban suka ba da tabbacin za su taimaka wa kasar nan a fannonin da suka jibanci matakan tsaro da ta`addanci da yaki da cin hanci da rashawa da sauran matsalolin da ya gada daga gwamnatin PDP ta tsohon shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan.
 A yunkurinsa na kawo karshen gwagwarmayar `yan kungiyar Boko Haram, `yan kungiyar da gwagwarmayarsu take cikin shekaru shida, wadda kuma zuwa yanzu ta tsallaka zuwa kasashen makwabtanmu, irin su Jamhuriyar Nijar da Chadi da Kamaru da Benin, a cikin wadannan kwanaki 100, da ake magana Shugaba Buhari ya samu ziyartar dukkan wadancan kasashe, inda ya gana da shugabanninsu, wasu ma har sau biyu, akan yadda za a kawo karshen wannan annoba, ta hanyar tunkarar yakin tare, wanda zuwa yanzu duk kasashen sun amince da tabbatar da kafuwar Rundunar karo-karon askarawa Dubu takwas da.700.
A nan cikin gida kuma saboda irin gambawul din da ya yi na canja manyan Hafsoshin Dakarun kasar nan da kokarin wadata su da makamai da sauran kayayyakin aiki, tun da Shugaba Buhari ya ba su wa`adin nan da karshen wannan shekarar da lallai su tabbatar da sun kawo karshen gwagwarmayar ta `yan Boko Haram din, umurnin da manyan Hafsoshin soja suka sha alwashin cikawa.
Ta fannin batun farfado da tattalin arzikin kasa kuwa, tuni Shugaba Buhari ya sauke manyan jami`an da suke kula da Hukumomim gwamnatin tarayya da suke kawo kudin shigar kasar nan mafi tsoka, irin su Kamfanin man fetur na kasa, wato NNPC da na Hukumar tara kudin haraji ta kasa, wato FIRS da na Hukumar hana fasa kwauri, sannan kuma ya ba da umurnin a koma tsarin yin ajiya daya tak akan dukkan kudin shigar gwamnatin tarayya, kuma da Babban Banki kasa, sabanin yadda ake a da, asusun ajiyar Ma`aikatu da Hukumomin gwamnatin tarayya su ke barkatai a bankunan kasuwancin kasar nan. Daga dukkan alamu kuma dukkan irin jami`an da Shugaba Buhari ya nada su maye gurbin wadanda ya sauke, ko su `yan adawa da sauran kungiyoyin wasu kabilun Kudancin kasar nan da wasu daidaikun `yan kasa, da suke kokawa akan nade-naden, ba suna kokawa ba ne akan rashin nagartar wadanda aka nada, sai don mafi yawansu sun fito ne daga Arewacin kasar nan. Koke-koken da tuni Shugaba Buhari ya ce za a gyara.
Mai karatu akwai sauran bayanai akan rawar da gwamnatin ta fara takawa a cikin wadannan kwanaki 100, irin su ingantuwar wutar lantarki da tsarin aikin gwamnati da babban yakinsa na cin hanci da rashawa da dai sauransu da karancin fili ba zai bari in kawo su ba. Babban abin so a gani daga gwamnati, shi ne lallai ta tabbatar da cewa komai za ta yi, to ta yi adalci, ga `yan kasa kuma hakuri da addu`o`i ga masu mulki.  Don ko yanzu an ga kamun ludayin jagorancin Shugaba Buhari