Kan wakilan PDP a majalisa ya rabu kan yunkurin tsige Tambuwal
Akwai alamun cewa kan wakilan Jam’iyyar PDP a Majalisar Tarayya ya rabu game da yunkurin tsige Shugaban Majalisar Alhaji Aminu Waziri Tambuwal. Jam’iyyar PDP da Fadar Shugaban kasa suna ta matsa wa Aminu Tambuwal kan ya sauka daga kujerarsa bayan da ya koma Jam’iyyar APC a ranar 28 ga Oktoban da ya gabata. Majalisar dai […]
Akwai alamun cewa kan wakilan Jam’iyyar PDP a Majalisar Tarayya ya rabu game da yunkurin tsige Shugaban Majalisar Alhaji Aminu Waziri Tambuwal.
Jam’iyyar PDP da Fadar Shugaban kasa suna ta matsa wa Aminu Tambuwal kan ya sauka daga kujerarsa bayan da ya koma Jam’iyyar APC a ranar 28 ga Oktoban da ya gabata. Majalisar dai ta dage zamanta zuwa 3 ga Disamba.
Sakamakon fusata matakin da Tambuwal ya dauka, an ruwaito cewa Jam’iyyar PDP ta umarci wakilanta su kira zaman majalisar a wani yunkuri na tsige shugaban. Umarnin ya biyo bayan ganawa a tsakanin jam’iyyar da shugabannin majalisar.
Sai dai wakilan sun bukaci uwar Jam’iyyar PDP ta ba su tikitin takarar kai-tsaye kafin su fara shirin tsige shugaban.
Kuma umarnin da PDP ta fitar a ranar Litinin cewa kowa na da damar sayen fom domin tsayawa takarar kowane mukamai, sai wasu wakilan suka ce ba za su sanya hannu a tsige shugaban nasu ba.
Baya ga haka, bayanai sun nuna cewa an riga an yi waje da wasu wakilan sakamakon zakudawa da kujerun zuwa wasu yankunan kananan hukumomi a jihohinsu.
Bayanai sun ce wasu daga cikin wakilan PDP a majalisar ma suna jira ne majalisar ta dawo inda za su bayyana komawarsu Jam’iyyar APC tunda babu abin da za su amfana daga jam’iyyar.
Wata majiya ta shaida wa wakilinmu cewa: “Duba, babu wanda zai ci gaba da batun tsige Tambuwal. Idan jam’iyya ba za ta yi wa wakilai abin da suke so ba, to babu dalilin ci gaba da wannan yunkuri.”
Wata majiyar ta ce koda jam’iyyar ta ba su tabbacin tikiti kai-tsaye, wasu wakilan ba za su ci gajiyar haka ba, domin tuni an maye gurbinsu da wasu, don haka ba za su amince da umarnin jam’iyyar na bude majalisar kafin hutun ba.
Akwai bayanan da ke nuna cewa wasu magoya bayan PDP suna matukar goyon bayan Tambuwal din.
Alhaji Aminu Tambuwal ya hadu da matsaloli da dama bayan komawarsa APC, ciki har da janye jami’an tsaronsa da Sufeto Janar na ’yan Sandan Najeriya Suleiman Abba ya yi, kuma bayan janye su ne Jam’iyyar PDP ta fara shirin tsige shi.
Tuni shugaban majalisar ya garzaya wata babbar kotu a Abuja inda ya bukaci ta hana PDP ko Fadar Shugaban kasa ko wani wakilinsu daga bude zaman majalisar ko tsige shi daga mukaminsa.
A takardar rantsuwa da ya gabatar a gaban Babbar Kotun Tarayya ta Abuja, Tambuwal ya zargi Shugaban Jam’iyyar PDP ta kasa Ahmadu Adamu Mu’azu da Mataimakin Shugaban Majalisar Tarayya, Emeka Ihedioha da Ministan Shari’a Mohammed Bello Adoke da yunkurin kiran zaman majalisar domin tsige shi, kuma ya bukaci kotun ta hana bude zaman majalisar sai ranar 3 ga Disamba.
Alkalin Kotun Mai shari’a Ahmed Mohammed ya amince da bukatar zuwa yau da kotun za ta fara sauraron karar.