Kanada ta ba Najeriya tallafin Naira miliyan 10

Gwamnatin kasar Kanada ta bada gudummawar Dalar Amurka Naira miliyan goma domin tallafa wa shirin inganta lafiyar yara da mata masu juna biyu.Jakadan kasar a Nijeriya, Mista Perry Calderwood shi ne ya sanar da haka wajen wata liyafa da aka shirya bayan kammala wani taron kara wa juna sani kan  ci gaban Nahiyar Afirka da […]

Kanada ta ba Najeriya tallafin Naira miliyan 10
Kanada ta ba Najeriya tallafin Naira miliyan 10

Gwamnatin kasar Kanada ta bada gudummawar Dalar Amurka Naira miliyan goma domin tallafa wa shirin inganta lafiyar yara da mata masu juna biyu.
Jakadan kasar a Nijeriya, Mista Perry Calderwood shi ne ya sanar da haka wajen wata liyafa da aka shirya bayan kammala wani taron kara wa juna sani kan  ci gaban Nahiyar Afirka da aka gudanar a Jami’ar Bayero, inda ya bayyana cewa Nijeriya tana cikin sahun farko wajen yawan yara masu tamowa da kuma matsalolin da ake samu  wajen haihuwa da kuma laulayin ciki.
Ya kara da cewa gwamnatin  Kanada tana kokari  wajen bai wa kasashen duniya tallafi  musamman ta fannin kula da lafiya ta hannun kungiyar UNICEF da kuma wasu kungiyoyi amintattu wadanda kuma suke aiki a fannin kula da lafiya.
Mista Perry ya kuma sanar da cewa shirin tallafa wa yaran zai dauki shekaru biyar, sannan za a fadada shi zuwa jihohin Bauchi da Katsina da kuma sauran jihohi makwabta kana za a ci gaba da  tafiyar da wannan shiri ne a bisa jagorancin wata kungiya a kasar nan.