‘kananan hukumomin Bauchi 10 ba su samun jaridar Aminiya’

kananan hukumomi 10 daga cikin 20 da ke Jihar Bauchi ba su samun jaridar Aminiya kamar yadda binciken wakilinmu ya gano. Wani mai sayar da jaridu mai suna Usman Bendo da ke karamar Hukumar Katagum ya bayyana wa wakilinmu cewa yakan samu koke-koke daga kananan hukumomin Shira da Zaki da Damban da Itas Gadau da […]

‘kananan hukumomin Bauchi 10 ba su samun jaridar Aminiya’
‘kananan hukumomin Bauchi 10 ba su samun jaridar Aminiya’

kananan hukumomi 10 daga cikin 20 da ke Jihar Bauchi ba su samun jaridar Aminiya kamar yadda binciken wakilinmu ya gano. Wani mai sayar da jaridu mai suna Usman Bendo da ke karamar Hukumar Katagum ya bayyana wa wakilinmu cewa yakan samu koke-koke daga kananan hukumomin Shira da Zaki da Damban da Itas Gadau da Gamawa daWarji da sauransu. Don haka ya yi kira ga mahukuntan kamfanin Media Trust mai buga jaridun Trust da Aminiya su dubi wannan lamari su share musu hawaye. Sauran kananan hukumomin da ba sa samun Aminiya sunhada da bogoro da Kirfi da Darazo da Alkaleri kamar yadda Alhaji Sama’ila Maigwanjo ya bayyana wa wakilinmu a garin Alkaleri. Mista Habila danrimi daga karamar Hukumar bogoro ya ce rabonsa da ya ga Aminiya a garinsu ya shafe sama da shekara uku. Sai dai ya aika garin Bauchi a sayo masa jaridun Hausa da suka hada da Aminiya da Leadership Hausa da Rariya.