kananan Hukumomin Roni da Yankwashi sun ciri tuta a Jigawa
kananan Hukumomin Roni da Yankwashi dake a Jahar Jigawa sun ciri tuta bisa ayyukan raya kasa da jama’a, inda karamar Hukumar Yankwashi ta samar da kujerun makaranta guda 350 masu daukar dalibai uku da nufin samar da isassun kayan zama a daukacin makarantun yankin a kokarin karamar hukumar na inganta harkokin koyo da koyarwa a […]

kananan Hukumomin Roni da Yankwashi dake a Jahar Jigawa sun ciri tuta bisa ayyukan raya kasa da jama’a, inda karamar Hukumar Yankwashi ta samar da kujerun makaranta guda 350 masu daukar dalibai uku da nufin samar da isassun kayan zama a daukacin makarantun yankin a kokarin karamar hukumar na inganta harkokin koyo da koyarwa a daukacin makarantun yankin.
Shugaban karamar hukumar ta Yankwashi, Alhaji Dauda Dan-Auwa ya shaida wa manema labarai haka a makon da ya gabata, ya ce sun raba kujeru 150 a makarantun firamare dake yankin yayin da suka raba guda 200 ga makarantun kananan sanakadire dake karamar hukumar.
Dan-Auwa ya ci gaba da cewar sun sayi littafan rubutu guda dubu 12 wadanda aka rabawa dalibai musamman wadanda iyayensu ba su da karfi, ya kara da cewar karamar hukumar ta gina fanfunan tuka-tuka guda 30 da rijiyoyin ruwan sha uku a kauyan Sada da Zoto da Unguwar Tudu cikin wata hudu da hawansu don wadata al’ummar yankin da ruwan sha. Ya kara da cewa karamar hukumar c eke daukar nauyin dakowa da mayar da daliban, sannan ita ke daukar nauyin maganain daliban kyauta.
Haka kuma ya ce karamar hukumar ta samar da gadaje da katifu da man da ake sawa a injinan bada ruwan sha, sannan ta kashe sama da naira miliyan guda da rabi wajen sayan kayan gyaran tuka-tuka da na injinan bada ruwan sha masu aiki da hasken rana da kuma masu amfani da mai.
Haka kuma karamar Hukumar Roni ta sayi kekunan saka guda 15 da kuma na koyawa mata dinki guda biyar wadanda aka kafa su a cibiyar koyawa mata sana’a a karamar hukumar domin mata su zama masu dogaro da kansu a yankin, kuma yanzu haka ta sayi karin kekunan dinki hudu wadanda za ta kafasu a kauyen Amaryawa a matsayin cibiyar horas da mata.
Shugaban karamar Hukumar ta Roni, Alhaji Sani Salisu ya sanar da taron manema labarai haka a makon nan, inda ya ce karamar hukumar ta yi wa kungiyoyin mata 31 rijista da nufin taimakawa matan dake karamar hukumar su zama masu dogaro da kansu.
Ya ce yanzu haka sun yi wa mata 465 rijista domin koyar da su sana’a kuma za a fara gwadawa matan sana’ar yin cincin da makamantansu, an zakulo matan ne daga mazabu 11 na yankunan karamar hukumar.
Ya ci gaba da cewar an sayi tabarmi 250 an rabawa mazabun 11 dake karamar hukumar, wadda aka bawa masallatai da makarantun islamiyya.
Da ya juya wajen ayyukan addini, ya ce sun sayi makara manya da kanana sun raba a daukacin mazabun yankin da nufin saukakawa jama’a wahala a lokacin da aka yi rasuwa, saboda wasu masallatan babu makara a cikinsu. Haka nan ya ce karamar hukumar ta taimakawa kungiyoyin masu dafa shayi da kayan sana’a tare da ba su jari da nufin inganta harkokinsu, haka zalika karamar hukumar ta gwadawa mata yadda ake yin garin bonbita da sabulun wanki tare da man shafawa.
“Sannan karamar hukumarmu ta taimakawa masu larurar hauka mutun 34 haka nan ayyukan motsa mun gina filin wasan kwallon kwando da kwallon hannu. Sai kuma kayan amsa kuwwa a daukacin masallatan yankin ,” a cewarsa.
Da ya juya wajen ayyukan gyaran mahalli da kungioyoyin aikin gayya, ya ce karamar hukumar ta amsa kiran da gwamnatin jahar ta yi na a dawo da aikin tsaftar mahalli, inda ta amshi naira miliyan biyu daga gwamnatin jahar wajen farfado da ayyukan tsaftar mahalli.
Shi kuwa kakakin karamar hukumar ta Roni, Malam Bello Muhammed ya ce karamar hukumar zata gina hanyoyin mota a shekara mai zuwa daga Fara zuwa Bashe da kuma Jigawa zuwa dabawa da kuma hanyar Yarsara zuwa Roni ta zarce zuwa Gada.
Ya kara da cewar burin karamar hukumar a shekara mai zuwa zasu mayar da hankali ne wajen inganta rayuwar mazauna karkara ta hanyar samar da wutar lantarki da ruwan sha da inganta hanyoyin sufiri da sauransu.