kananan hukumomin Taraba sun saye kamfanin ganyen shayi na Mambilla

kananan hukumomin Jihar Taraba 16 sun saye kamfanin sarrafa ganyen shayi na Mambilla da ke jihar. Mai baiwa Gwamnan Jihar shawara kan harkokin kananan hukumomi, Alhaji Bashir Marafa ne ya bayyana haka a lokacin yake mika aiki ga wanda ya gaje shi.Alhaji Bashir Marafa wanda ya ajiye aikinsa don yin takarar Sanata daga Taraba ta […]

kananan hukumomin Taraba sun saye kamfanin ganyen shayi na Mambilla
kananan hukumomin Taraba sun saye kamfanin ganyen shayi na Mambilla

kananan hukumomin Jihar Taraba 16 sun saye kamfanin sarrafa ganyen shayi na Mambilla da ke jihar.

Mai baiwa Gwamnan Jihar shawara kan harkokin kananan hukumomi, Alhaji Bashir Marafa ne ya bayyana haka a lokacin yake mika aiki ga wanda ya gaje shi.
Alhaji Bashir Marafa wanda ya ajiye aikinsa don yin takarar Sanata daga Taraba ta Tsakiya ya ce sayen kamfanin ganyen shayin da kananan hukumomin suka yi na daya daga cikin nasarorin da ya samu a lokacinsa.
Ya ce kamfanin wanda ya durkushe kafin kananan hukumomi su saye shi zai taimaka wajen sake farfado da kamfanin kuma ya samar da ayyukan yi ga matasan kananan hukumomin jihar.
Alhaji Marafa ya ce a lokacinsa an gina tituna masu tsawo kilomita hudu a kowace karamar hukumar jihar, kuma kananan hukumomin sun sayi jirgin sama na sufuri wanda da zarar an kammala aikin fadada filin jirgin saman garin Jalingo zai fara jigilar fasinja daga Jalingo zuwa Abuja da sauran sassan kasar nan.
Alhaji Marafa ya ce a lokacinsa ne aka fara biyan ma’aikatan kananan hukumomin jihar sabon albashin Naira dubu 16.
A jawabin magajinsa kuma Babban Sakataren Ma’aikatar Alhaji Bello Yero ya yaba kyakkyawan shugabancin da Alhaji Marafa ya gudanar, ya ce ma’aikatansa da na kananan hukumomin jihar sun amfana da ayyuka nagari na tsohon mai bai wa Gwamnan Shawara.

KADVS ta daƙile yunƙurin sace yara da ceto wasu a Zariya

Gwamnatin Tinubu na yunƙurin hana ni yin takara — Peter Obi

An gurfanar da ƙarin mutum 17 bisa zarginsu a kisan malama

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi