Kananan hukumomin Zuru da Dandi sun fara ayyukan sam-barka
Shugaban karamar Hukumar Zuru da ke Jihar Kebbi, Alhaji Muhammadu Kabir Abubakar ya yi wa takwarorinsa zarra a fagen gudanar da ayyukan raya kasa a bisa kididdigar da ’yan jarida da suka ziyarci kananan hukumomi don tantance ayyukansu da suka fara yi a cikin kankanin lokaci da suka yi a kan kujerunsu. Shugaban karamar hukumar […]
Shugaban karamar Hukumar Zuru da ke Jihar Kebbi, Alhaji Muhammadu Kabir Abubakar ya yi wa takwarorinsa zarra a fagen gudanar da ayyukan raya kasa a bisa kididdigar da ’yan jarida da suka ziyarci kananan hukumomi don tantance ayyukansu da suka fara yi a cikin kankanin lokaci da suka yi a kan kujerunsu.
Shugaban karamar hukumar ne ya tabbatar da wannan batu, a yayin zantawar da ya yi da manema labarai a ofishinsa da ke hedikwatar karamar hukumar a garin Zuru.
Muhammadu Kabir Abubakar ya ce, ayyukan da suka aiwatar ga jama’arsu a ’yan watannin da suka yi a shugabancin karamar hukumar, ya ce da zuwansu sun fara gyaran manyan motocin yin aikin hanya da kuma na kwashe shara, sun kuma gyara masallatai biyu wanda ke cikin harabar karamar hukuma da kumadaya da ke kan hanyar zuwa Koko, inda ake tsayawa ana tarbo baki in za su shigo Zuru.
Alhaji Kabir Abubakar ya ci gaba da cewa sun gyara ofisoshin Shugaban karamar Hukumar da na Mataimakinsa da na Sakatare da na kansiloli da kuma gidan masu hidimar kasa (NYSC), sun kuma kirkiro hanyoyi domin samun kudaden shiga ga karamar hukumar saboda yi wa jama’ar yankin aiki da kudinsu.
Da ya koma ta bangaren tsaro, ya ce sun kara inganta aikin ’yan sintiri wajen samar musu da kayan aiki da kuma biyansu hakokkinsu. A karshe shugaban karamar hukumar ya ce, ita ma Gwamnatin Jihar Kebbi ta giggina musu hanyoyi daga Dabai zuwa Zuru da kuma hanyar Dabai zuwa Koko, sai hanyar Zuru zuwa Ribah zuwa Wasagu.
Shi ma Shugaban karamar Hukumar Dandi-Kamba Alhaji Garba Salihu Dila Kamba, ya ce cikin ’yan watannin da suka yi sun dukufa wajen ayyukan raya karkara a yankinsa, inda ya ce da hawansu ba abin da ya fara yi sai gyaran famfunan burtsatse da rijiyoyi masu amfani da hasken rana. Kuma ya ce, garuruwan da suka samu damar gyara masu rijiyoyin burtsatsen sun hada da garin Kamba da Tunkari kato da Tukurwa da Doma da Tungar Rafi, ya c wadannan ayyuka da suka fara suna daga cikin alkawuran da suka yi wa jama’a a lokacin yakin neman zabe, ya kuma ce wannan somin- tabi ne.
Shi ma a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishin sa, shugaban karamar hukumar Maiyama, Hon. Maidamma Magaji Dogon Daji, ya ce zai mayar da hankali wajen samar da ingantattun hanyoyi tare da ruwan sha da ilimi da kiwon lafiya da kuma yakar cututtukan dake halaka kananan yara.
Ya ce duk da cewa wannan ne karo na farko da ya zama zababben shugaban karamar hukumar, ya yi alwashin samar da isasshen tsaro ga al’ummar yankin da kuma bada tallafi a fannin noma musamman noman rani, ya kuma ce za a fara tura ma’aikata zuwa yin kwasa-kwasai domin sanin makamar aiki wadansu kuma a tura su zuwa makaranta domin karo ilimi.