kananan kabilu sun ce kada gwamnatin Buhari ta yi wa ’yan tawayen Neja Delta afuwa
kungiyar kananan kabilun Nijeriya ta yi kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari da kada ya kuskura ya yi wa ’ya’yan kungiyar Niger Delta Abengers da suke kai hare hare ga bututun mai a yankin Neja Delta afuwa. kungiyar ta yi wannan kira ne a wajen wani taron ’yan jarida da ta kira a garin Jos […]
kungiyar kananan kabilun Nijeriya ta yi kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari da kada ya kuskura ya yi wa ’ya’yan kungiyar Niger Delta Abengers da suke kai hare hare ga bututun mai a yankin Neja Delta afuwa.
kungiyar ta yi wannan kira ne a wajen wani taron ’yan jarida da ta kira a garin Jos fadar Jihar Filato, inda shugaban kungiyar Mista Okpokwu Ogeyi ya ce bai kamata gwamnatin Buhari ta yi wa wadannan tsageru afuwa ba, maimakon hana ya kamata gwamnatin ta tashi tsaye ta magance hare-haren da ’yan tawaye suke kaiwa. Ya ce “Idan gwamnati ba ta tashi ta magance ayyukan ’yan ta’adda ba, za su iya kawo mata cikas kan kudirorin da ta sanya a gaba na bunkasa kasar nan. Mun fahimci wadannan ’yan tawaye suna kokarin dakile himmar da wannan gwamnati take yi, na gyara kasar nan, don su hana ta binciken da take yi a kan irin almundahanar da iyayen gidansu suka aikata ne a gwamnatin baya.”
Mista Ogeyi ya yi zargin cewa daga lokacin da ’yan kungiyar Niger Delta Abengers suka fara kai hare-hare zuwa yanzu sun lalata rijiyoyin mai da bututun mai masu yawa tare da kashe jami’an tsaro sama da 50, a yankin Neja Delta.
Ya ce ayyukansu zai iya kawo rashin zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya, don haka sun yi kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari da jami’an tsaro su tashi tsaye su magance ayyukan ’yan tawayen kamar yadda suka yi wa ’yan kungiyar Boko haram.