Kananan ’yan kasuwa dubu 150 da mata dubu 22 sun samu bashi mai sauki a bara

A ranar 30 ga watan Mayun shekarar 2017, Mukaddashin Shugaban Kasa a lokacin, Farfesa Yemi Osinbajo ya amince da kudirin dokar samar da hada-hadar bashi kan kananan kadarori. Kodayake Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanya ka’idojin kafa sashen kadarori da jingina amma babu wata doka a kan lamarin. Kudirin dokar tattala jingina ta kara kyautata […]

Kananan ’yan kasuwa dubu 150 da mata dubu 22 sun samu bashi mai sauki a bara
Kananan ’yan kasuwa dubu 150 da mata dubu 22 sun samu bashi mai sauki a bara

A ranar 30 ga watan Mayun shekarar 2017, Mukaddashin Shugaban Kasa a lokacin, Farfesa Yemi Osinbajo ya amince da kudirin dokar samar da hada-hadar bashi kan kananan kadarori.

Kodayake Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanya ka’idojin kafa sashen kadarori da jingina amma babu wata doka a kan lamarin.

Kudirin dokar tattala jingina ta kara kyautata ka’idojin da Bankin CBN ya sanya tare da tabbatar da tsarin.

Kudirin dokar na son cimma tattarawa da tattala riba dangane da kananan kadarori ta hanyar karfafa hada-hadar kuxi ta bai-xaya a Najeriya don saukaka samar da bashi ga kananan ’yan kasuwa da kuma saukaka musu samun bashi da kananan kadarori.

Bayan shekara biyu, kididdigar da Aminiya ta gani kwanan nan daga Hukumar Tattala Jingina ta Kasa (NCR) ta nuna cewa ’yan kasuwa dubu 154 da 827 suka yi amfani da kananan kadarorinsu suka karbi bashi daga hukumomin kuxi, daga cikinsu kimanin dubu 22 da 251 mata ne.

Kididdigar ta nuna cewa masu neman bashi sun samu kuxi daga hukumomin kuxi a bara ta hanyar amfani da kadarorinsu a matsayin jingina. Mafi yawan waxanda suka samu bashin a shekarar 2017 ya nuna karuwar shigar kananan manoma da ke karkashin shirin bayar da bashi na Bankin CBN waxanda suka samu bashin ta tsari mafi sauki.

Kididdigar ta nuna cewa karin da aka samu an danganta shi da samun karin kananan bankuna a na’urar Hukumar NCR da kuma karin masu ajiyar kuxi a bankuna da cibiyoyin kuxi da ba na bankuna ba.

Daga cikin jimillar Naira tiriliyan xaya da biliyan 209 da miliyan 381 da dubu 633 da kwabo 90, kimanin Naira biliyan 43 da miliyan 618 da dubu 262 da 792 da kwabo 17 mata aka baiwa.

Wannan ci gaba yana da mutukar muhimmanci saboda  abubuwa uku, tattala bayanan kwarewar hada-hadar kuxi da alaka mai karfi a tsakanin bankuna da kuma karkon jinginar su ne suka rage haxarin asarar da za a iya fuskanta wanda mai bayar da bashi zai yi amfani da su wajen lura sosai yayin da bayar da bashi.

Mafi yawan kananan ’yan kasuwa da kyar suka jure wa lamarin a shekara biyar na farko da suka yi saboda karancin jari. Kuxi suna da mutukar muhimmanci wajen  gudanar da kasuwanci cikin nasara.

Kanana ’yan kasuwa suna kasa karbar bashi daga bankuna saboda ka’idoji masu tsauri na kadarar da za a bayar a matsayin jingina da kuma yadda bankuna suka fi bayar da fifiko kan kadarar fili a matsayin kadarar jingina kuma irin waxannan filaye dole su zama suna da takardar mallaka ta gwamnati da kuma amincewar Gwamnan Jihar da filin yake. Wannan ka’idoji masu tsauri su ne suke hana kananan ’yan kasuwa samun bashi.

Kudirin dokar ’yancin jingina wata dabara ce da za ta magance matsalolin hada-hadar kuxi wacce mai asusun ajiya zai samu saukin karbar bashi cikin kwanciyar hankali.

Wannan tsari zai taimaka wa mai karbar bashi ya yi amfani da kananan kadarori da kuma sauran kadarori a matsayin abin da zai iya bayar da jingina a ba shi bashi kuma hakan zai kara inganta samun bashi saboda kananan kadarori da sauran kadarori za su kasance su ne jarin kamfanoni hakan kuma ya haxa da tarin jarin da kananan ’yan kasuwa suke da shi.

Kananan kadarori su ne kadarorin da kananan ’yan kasuwa za su iya bayarwa jingina musamman a kasashe masu tasowa za su iya samun bashi da samun damarmaki a harkokin noma da sauransu. Hukumar tattala jingina za ta bai wa manoman Najeriya da ’yan kasuwa damar samun kuxi da kadara wacce masu bayar da bashi za su damu da ita a matsayin kadarar jingina.

Karamar kadara karkashin sashen tattala ka’idojin kadara ta haxa da kayayyaki, asusun ajiya da kayan amfanin gida da asusun banki da kayan noma da ababen hawa da jirgin ruwa da jirgin sama da kayayyakin yau da kullum da bishiyoyin da ake kula da su da mai gas da albarkatun kasar da aka tono da makamantansu.

Jim kaxan bayan kammala taron kwamitin bankuna, Manajan Darakta kuma Babban Jami’in Bankin Union, Emeka Emuwa da yake jawabi a madadin kwamitin ya ce masu ruwa-da-tsaki sun bayyana cewa a yanzu lokaci ya yi da kananan ’yan kasuwa za su haxa kansu don samun bashi wanda zai sanya su bayar da tasu gudunmawar wajen samar da ayyukan yi.

Emuwa ya ce: “Ya zama wajibi kannana ’yan kasuwa su yi amfani da damar tsarin tattala kadara don haxa kansu wuri xaya don samun bashi daga hukumomin kuxi”.

Shawarar da kwamitin bakuna ya bayar ba a bar watsi ba ce. Cin nasarar xan kasuwa wajen samun bashi ya dogara ne da kokarinsa na rage asara da masu bashin suke yi ga kananan ’yan kasuwa.

Saboda haka, shawarar da kwamitin bankuna ya bayar tana kan gaba dangane da rawar da Sashen Tattala Jingina na Kasa ya taka wanda wani tsari ne da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bullo da shi don karfafa samun kuxi ga kanana da matsakaitan ’yan kasuwa.

Saboda haka ya zama wajibi a san cewa masu neman bashi kimanin dubu 16 da 349 suka nemi bashi ta yanar gizon Sashen NCR a bara saboda karin masu neman bashi da kananan kadarori da kuma wayar da kan jama’a da aka yi.

Sashen NCR ya nuna cewa mataki na gaba shi ne shirya taron bita na kwanaki biyu zuwa uku da haxin gwiwar Bankin Duniya da Cibiyar Shari’a ta Kasa ga Ma’aikatan Shari’a kan samun bashi da kananan kadarori a matsayin na Najeriya.

Sashen ya yi tsarin shirya lacca da taron wayar da kan lauyoyi da ’yan sanda da cibiyoyin hada-hadar kuxi kan bayar da bashi da kananan kadarori da kuma yadda za a tattala tsarin jingina da kashi 50 cikin  100 na bankuna masu rajista da sauran cibiyoyin hada-hadar kuxi.