kananan ’yan kasuwa sun dawo da sayen kaya a yankin Ibo
kungiyar kananan ‘yan kasuwar arewacin Najeriya da suke zuwa Kudancin Najeriya, sayo kayayyaki sun dakatar da sanarwar janyewa zuwa yankin Ibo sayen kayayyaki, da suka bayar kwanakin baya, sakamakon rikicin da aka yi kan fafutukar neman kasar Biyafara kwanakin baya, wanda ya yi sanadin asarar rayuka da dukiyoyin ’yan kungiyar. kungiyar ta dakatar da wannan […]
kungiyar kananan ‘yan kasuwar arewacin Najeriya da suke zuwa Kudancin Najeriya, sayo kayayyaki sun dakatar da sanarwar janyewa zuwa yankin Ibo sayen kayayyaki, da suka bayar kwanakin baya, sakamakon rikicin da aka yi kan fafutukar neman kasar Biyafara kwanakin baya, wanda ya yi sanadin asarar rayuka da dukiyoyin ’yan kungiyar.
kungiyar ta dakatar da wannan janyewa ne a ranar Lahadin nan da ta gabata, bayan da ta yi taro da Gwamnatin Jihar Abiya.
da yake yiwa jaridar Aminiya karin bayani dangane da wannan mataki da kungiyar ta dauka, sakataren kungiyar Alhaji Bashir Uba Hassan ya bayyana cewa, kamar yadda suka ba da sanarwar cewa duk wani dan kasuwa da yake zuwa yankin Ibo ya dakata, saboda abin da ya faru a Jihar Abiya kwanakin baya.
Ya ce bayan mun dakatar da ’yan kasuwar zuwa wannan yanki, sai ga sanarwa daga Gwamnatin Jihar Abiya tana neman mu je mu zauna mu tattauna kan wannan al’amari da ya faru.
Ya ce nan take suka sanar da shugabannin wannan kungiya na dukkan Jihohin Arewa 19 kan su turo da wakilansu domin mu je mu yi wannan zama da Gwamnatin Jihar Abiya.
“Mun hadu a garin Aba babban birnin jihar ta Abiya a ranar biyu ga watan 10 nan, muka tafi gidan gwamnatin jihar, inda muka zauna da mataimakin gwamnan jihar Mista Ude Ekochukwu. A wannan zama mun gabatar da korafe-korafen cewa rayukanmu da dukiyoyinmu ba su da wani mahimmanci a wajen mutanen wannan yanki, a duk lokacin da aka samu wani rikici. Saboda a duk lokacin da aka samu wani rikici a yankin ana kashe mana mutane, kamar abin da ya faru kwanakin baya. don haka bai kamata mu cigaba da daukar dukiyoyinmu da rayukanmu muna tafiya wannan yanki ba. Haka kuma mun gabatar da kukanmu kan irin takurawar da ake yi mana wajen karbar kudin haraji kan hanyoyiin wannan yanki.’’
Sakataren ya yi bayanin cewa mataimakin gwamnan ya ba da tabbacin cewa gwamnatin jihar za ta yi iyakar bakin kokarinta wajen ganin ta kiyaye hakkokin ’yan kasuwar, tare da duba al’amarin yawan kudin harajin da ake karba wajen ’yan kasuwar.
Sakataren ya ce ganin irin karbar da aka yi musu da tabbacin da gwamnatin jihar ta ba su na kare rayuka da dukiyoyinsu da zaman da gwamnatin jihar ta yi da shugabannin ’yan kasuwar wannan yanki na Ibo, sun janye dakatarwa da suka yi na zuwa yankin sayen kayayyaki.
Ya ce daga ranar Lahadin nan sun janye dakatarwa, yanzu kowanne dan kasuwarsu zai iya zuwa yanki sayo kayayyaki.