Kananan ‘yan kasuwar Arewa sun dakatar da zuwa yankin Ibo

Kungiyar kananan ‘yan kasuwar Arewacin Najeriya da suke zuwa kudancin Najeriya sayo kayayyaki sun bayyana cewa sun dakatar da zuwa yankin Ibo sayo kayayyaki, har sai an ba su tabbacin  za a kare rayuka da dukiyoyinsu. Shugaban kungiyar Alhaji Usman Baba Sa’idu ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da jaridar Aminiya. Ya […]

Kananan ‘yan kasuwar Arewa sun dakatar da zuwa yankin Ibo

Kungiyar kananan ‘yan kasuwar Arewacin Najeriya da suke zuwa kudancin Najeriya sayo kayayyaki sun bayyana cewa sun dakatar da zuwa yankin Ibo sayo kayayyaki, har sai an ba su tabbacin  za a kare rayuka da dukiyoyinsu. Shugaban kungiyar Alhaji Usman Baba Sa’idu ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da jaridar Aminiya.

Ya ce sun dauki wannan mataki ne sakamakon irin asarar rayukan mutanensu  da dukiyoyinsu da suka yi a lokacin da aka yi rikicin fafutukar neman kasar Biafara, makonni biyu da suka gabata.

Alhaji Usman Baba ya ci gaba da cewa wannan kungiya wadda ta hada kananan ‘yan kasuwar Arewa  da suke sayo kayayyakin kwalliya da yadi da takalma da zare da leda a yankin na Ibo, sun yanke wannan shawarar ce wajen tarurrukan da suka gudanar a garuruwan Kano da Jos.

Ya ce  za su cigaba da wannan dakatarwa har na tsawon kwanaki 14, kuma za su rubutawa ‘yan kasuwar da suke zuwa wajensu sayo kayayyaki, wannan kuka  na kare rayuka da dukiyoyinsu, domin su isar zuwa ga hukumominsu.

A ranar da wannan rikici ya faru akwai kanannan ‘yan kasuwa daga Arewa da suka je kasuwar Aba sayo kayayyaki,  da dama   har yanzu ba a ga wasu ba. Bai kamata ‘yan kasuwar da suke gudanar da harkokin kasuwanci a kasuwar Aba su bari a ci mutuncin ’yan kasuwar da suke zuwa  wajensu sayen kayayyaki  ba. Mu kananan ’yan kasuwa da ke nan Arewa muna tafiya da dukiyarmu zuwa yankin Ibo don sayo kayayyaki, a kullum muna cikin hadari. Kuma wannan abu da ya faru, ya sha faruwa, amma babu wani mataki da aka dauka. Don haka muka dauki wannan matsaya.’’

Ya yi kira ga kananan ‘yan kasuwar Arewa  da suke zuwa sayo kayayyaki kudancin kasar nan, musamman yankin Ibo su kiyaye rayukansu da dukiyoyinsu. Haka kuma ya yi kira ga ’yan kasuwar kudu  da ake sayo kayayyaki a wajensu, su dauki matakai na kare rayuka da dukiyoyin wadanda suke zuwa wajensu sayen kayayyaki.