Kanawa 19 sun mutu a hatsarin motar Dangote a Kogi

Hatsarin tirelar simintin Dangoten da wata bas ya yi sanadin mutuwar fasinjoji 19 da suka taso daga Kano a hanyar Lakwaja zuwa Okene

Kanawa 19 sun mutu a hatsarin motar Dangote a Kogi

Wani hatsarin mota

Akalla mutane 19 sun rasu bayan wata tirelar simintin kamfanin Dangote ta yi taho-mu-gama da wata bas mai dauke da fasinjoji daga Kano a kan hanyar Okene zuwa Lankwasa da ke Jihar Kogi.

Kakakin Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC), Jonas Agwu, ya ce, hatsarin motocin biyu ya yi sanadiyyar tashin gobara.

Jonas Agwu, ya ce, jami’an hukumar sun shafe awa uku kafin su kashe wutar, kuma an ceto mutum biyu da ransu, kuma an kai su Babban Asibitin Okene.

Ya bayyana cewa bas din, kirar Toyota Hiace tana kan hannunta ne lokacin da tirelar Dangoten da ta taso daga Fatakwal ta sha gaba wata mota da ke gabansa ba daidai ba.

A sakamakon haka tirelar ta yi karo gaba da gaba da bas din da ke zuwa daga Kano, dauke da mutane 22 dukkansu maza.

Jami’in ya kara da cewa za a gurfanar da direban simintin Dangoten a gaba kuliya.

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta