Kanawa masu dukiya ba su son fitar da zakka – Hukumar Zakka
Darakta Janar na Hukumar Zakka da Hubusi na Jihar Kano Alhaji Safiyanu Ibrahim Gwagwarwa ya bukaci mawadata a jihar su rika fitar da zakka, musamman ganin cewa jama’a da yawa kan fitar da zakkarsu a watan Ramadan.Alhaji Safiyanu Gwagwarwa ya bayyana haka ne a cikin shirin Barka da Hantsi na gidan Rediyon Freedom da ke […]
Darakta Janar na Hukumar Zakka da Hubusi na Jihar Kano Alhaji Safiyanu Ibrahim Gwagwarwa ya bukaci mawadata a jihar su rika fitar da zakka, musamman ganin cewa jama’a da yawa kan fitar da zakkarsu a watan Ramadan.
Alhaji Safiyanu Gwagwarwa ya bayyana haka ne a cikin shirin Barka da Hantsi na gidan Rediyon Freedom da ke Kano, inda ya koka kan yadda mutanen jihar ba su son fitar da zakka. Ya ce kididdiga ta nuna cewa kimanin mutum 2019 ne ya kamata su fitar da zakka a jihar, sai dai zuwa yanzu zakkar mutum biyar ce kawai ta zo hannun hukumar. “Muna da lissafin mutum 2019 wadanda ya kamata su fitar da zakka a jihar nan, sai dai zuwa yanzu mutum biyar ne kacal suka kawo mana zakkarsu. Don haka muna kira ga wadanda suka san Allah Ya hore musu dukiya su kawo zakkarsu ga hukumarmu ko su kira mu je mu amsa. Mun san cewa mutane da yawa sukan zabi watan Ramadan a matsayin watan fitar da zakkarsu, don taimaka wa al’umma. To mu ma kofar hukumarmu a bude take don karbar zakka daga wurin mawadata da kuma bayar da ita ga mabukata. Kullum mabukata suna zuwa hukumarmu baya ga wadanda muke da lissafinsu,” inji shi.
Alhaji Safiyanu Gwagwarwa ya kara da cewa “Wadansu daga cikin mawadatan ba su gane adadin lissafin yawan dukiyarsu da adadin da za su fitar daga ciki, don haka muna kira su rika tuntubar malamai a kan haka don ganin sun fitar da zakkar kamar yadda Allah Ya yi umarni.”
Ya yi kira ga mawadata su rika bayar da zakka ga wadanda Allah Ya yi umarnin a ba su, ba a mayar da lamarin biki a tsakanin mawadata ba.