‘Kande da Mayya’

Barkanmu da warhaka manyan gobe Da fatan alheri kuma kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin ‘Kande da Mayya’. Labarin ya kunshi yadda sata take sanya mutum shiga wani hali. A sha karatu lafiya.Taku; Amina Abdullahi ‘Kande da Mayya’ Mahaifiyar Kande ta yi gum, shiru take ji kuma ba ta ga alamar […]

‘Kande da Mayya’
‘Kande da Mayya’

Barkanmu da warhaka manyan gobe

Da fatan alheri kuma kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin ‘Kande da Mayya’. Labarin ya kunshi yadda sata take sanya mutum shiga wani hali. A sha karatu lafiya.
Taku; Amina Abdullahi

‘Kande da Mayya’

Mahaifiyar Kande ta yi gum, shiru take ji kuma ba ta ga alamar dawowar ‘yarta daga kasuwa ba. Ta tashi ta tafi wajen sarki ya ce da ita zai sa dogarai su yi shelar nemanta. Da haka aka fara neman Kande.
Kamar da wasa har shekaru goma suka yi amma ba wanda ya san inda Kande take. Mahaifiyarta ta shiga damuwa kwarai.  Sai ta shiga zuwa wajen malaman tsubbu tana kashe kudi ko za a gaya mata inda ‘yarta take. Ga shi tana yawan kashe kudi domin biyan masu yi mata duba.
Rannan sai ta je gidan wata mayya da ta gama tsubbace-tsubbacenta, sai ta ce da ita abin ya fi karfinta amma za ta kwatanta mata inda za ta. Ta ce da ita akwai wani koko a wani daji za ta ga an rubuta sunanta a cikin kokon da wuta tana ci a ciki. In har ta ga hakan sai ta kira sunan’yarta.
Bayan sati biyu, mahaifiyar Kande ta je  wajen wannan kokon. Tana shiga sai ta fara kiran sunan’yarta. Can sai ta ga sunanta a bangon kokon. Ta ci gaba da tafiya sai ta ga wata wuta tana ci . Can sai ta hadu da sarauniyar mayu ta ce da ita ‘yarta tana nan.Ita ce ta kama ‘yarta domin da ta aike ta kasuwa sai ta yi mata satar biskit da su minti. Shi ya sa ta kama ta.  Sai ta ba ta wani abu ta shafa mata a goshinta can sai Kande ta tashi suka rungumi juna da mahaifiyarta. Sai mahaifiyarta ta mutu. Kande ta shiga kuka sai sarauniyar mayu ta ce da Kande mahaifiyarki ta mutu ne sakamakon satar da kika yi mini. Ki tashi ki koma gida.