Kande da rago

Barkanmu da warhaka Manyan Gobe da fatar ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin ‘Kande da Rago’. Labarin ya yi gargadi ga masu yawan karya. A sha karatu lafiya:   Kande yarinya ce mai son jiki da kuma kiwa. A kullum babu abin da take yi illa ta ci abinci ta kwanta. […]

Kande da rago

Barkanmu da warhaka Manyan Gobe da fatar ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin ‘Kande da Rago’. Labarin ya yi gargadi ga masu yawan karya. A sha karatu lafiya:

 

Kande yarinya ce mai son jiki da kuma kiwa. A kullum babu abin da take yi illa ta ci abinci ta kwanta. Mahaifiyarta na kiwon wani rago wanda a kullum take kai shi bakin rafi ya sha ruwa.

Ran nan sai mahaifiyarta ta kwanta rashin lafiya har ta gagara fita daga cikin daki. Sai ta roki Kande ta kai ragon shan ruwa bakin rafi kamar yadda ta saba.

Kande ta ki, sai mahaifiyar ta ba ta kyautar alawa don ta kai ragon ya sha ruwa a bakin kogi domin a ranar an yi zafi sosai.

Kande na ganin alawa sai ta ja rago da nufin kai shi bakin kogi don ya sha ruwa.

Tana fita sai ta daure ragon a jikin wata bishiya ta zauna tana shan alawa. Rago ya kama kuka saboda kishi amma ko a jikinta.  Hasali ma tana gama shan alawar sai ta koma da rago gida ta yi wa mahaifiyartar karyar cewa rago ya sha ruwa.

Nan take abin ya ba rago haushi inda ya yi mata addu’ar ta makance.

Kwana kadan sai Kande ta makance, ta kasa fita ko’ina saboda rashin ido.  Da ta lura alhakin abin da ta yi ne ya kamata sai ta sanar da mahaifiyarta ainihin abin da ya faru kuma ta nemi a yafe mata amma bakin alkalami ya bushe.  Haka Kande ta ci gaba da rayuwa cikin kunci.

Da fatar Manyan Gobe za ku dauki darasi daga wannan labari.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos