Kane Tanaka: Tsohuwar da ta fi kowa yawan shekaru a duniya ta rasu

Tsohuwar ’yar asalin kasar Japan ta rasu tana da shekara 119

Kane Tanaka: Tsohuwar da ta fi kowa yawan shekaru a duniya ta rasu

Kane Tanaka. Hoto: Aljazeera

Kane Tanaka, tsohuwar nan ’yar asalin kasar Japan da aka yi ittifakin ta fi kowa yawan shekaru a duniya ta rasu tana da shekara 119.

Ta rasu ne a wani asibiti da ke birnin Fukuoka a Kudu maso Yammacin kasar ranar 19 ga watan Afrilu, kamar yadda kafar yada labaran kasar ta NHK ta rawaito ranar Litinin.

An dai haife ta ne a yankin ranar biyu ga watan Janairun 1903.

A shekarar 2019 ce kundin World Guinness Records ya tabbatar da ita a matsayin wacce ta fi kowa yawan shekaru a duniya.

Kafin rasuwarta dai, Tanaka ta kasance tana rayuwa a wani gidan gajiyayyu kuma tana cikin koshin lafiya in ban da a ’yan kwanakin bayan nan da jikinta ya yi zafi.

Ko a bara dai ta yi yunkurin shiga gasar Olympics amma daga baya ta fasa saboda annobar COVID-19.

Gwamnan yankin na Fukuoka, Seitaro Hattori, ya nuna kaduwarsa da rasuwar Tanaka, inda ya bayyana mutuwarta a matsayin babban rashi.

Kasar Japan dai tana da tarin tsofaffi inda yawan masu sama da shekara 65 ya kai kusan kaso 28 cikin 100.

Ya zuwa watan Satumban bara, kasar Japan na da kimanin mutum 86,510 da suka haura shekara 100, kuma tara daga cikin 10 na adadin mata ne.