kanen Shugaban Media Trust ya rasu
A yammacin Litinin da ta gabata ne Allah Ya yi wa Alhaji Abubakar Abdullahi Yusuf rasuwa, wanda kane ne ga Shugaban Kamfanin Media Trust, masu buga jaridun Aminiya da Daily Trust da Weekly Trust da Sunday Trust; Malam Kabiru Yusuf.Marigayin ya rasu ne da misalin karfe 2:10 na yamma a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu […]

A yammacin Litinin da ta gabata ne Allah Ya yi wa Alhaji Abubakar Abdullahi Yusuf rasuwa, wanda kane ne ga Shugaban Kamfanin Media Trust, masu buga jaridun Aminiya da Daily Trust da Weekly Trust da Sunday Trust; Malam Kabiru Yusuf.
Marigayin ya rasu ne da misalin karfe 2:10 na yamma a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, sakamakon ’yar gajeriyar rashin lafiya.
Kafin rasuwar marigayin, ma’aikaci ne a Kamfanin BUA. Haka kuma ya rasu yana da shekaru 50 da haihuwa, inda ya bar mata daya da ’ya’ya biyar.
Tuni dai aka binne mamacin kamar yadda addinin Musulunci ya tanada. Daga cikin wadanda suka halarci jana’izar marigayin sun hada da darakta a kamfanin Media Trust, Malam Umar Abdullahi da kuma babban manaja a kamfanin, Malam Sulaiman Sahabi da Iyan Katsina, Hakimin Mashi, Alhaji Kabiru Ahmed da tsohon Mataimakin Shugaban Hukumar Kwastam na kasa, Alhaji Muhamamd Tukur Bello da kuma wani na kusa da marigayin mai suna Alhaji Idiris Yusuf da sauran jama’a da dama.