kanin Amir Khan Hyder Khan ya samu shiga fim

A makon da ya gabata ne dandalin shirya fina-finai a Indiya (Bollywood) ya sake samun karuwa, inda labari ya bayyana cewa kanin shahararren dan fim Amir Khan, Hyder Khan ya zama dan wasa, inda ya fara fara fitowa a fim a karon farko.Kamar yadda aka tabbatar, Hyder Khan zai fara wasa ne da sabon fim […]

kanin Amir Khan Hyder Khan ya samu shiga fim

A makon da ya gabata ne dandalin shirya fina-finai a Indiya (Bollywood) ya sake samun karuwa, inda labari ya bayyana cewa kanin shahararren dan fim Amir Khan, Hyder Khan ya zama dan wasa, inda ya fara fara fitowa a fim a karon farko.
Kamar yadda aka tabbatar, Hyder Khan zai fara wasa ne da sabon fim mai suna ‘Dil Toh Dewaana Hai.’
Haka kuma fitaceen mai rubuta wakokin fina-finan Arbind Kejriwal, shi ne ya rubuta wakokin da sabon dan wasan zai rera a sabon fim din da ake kan shiryawa a halin yanzu.
Shi dai Hyder Khan da ne ga marigayi Tahir Hussain, wanda ya haifa tare da matarsa ta biyu, kishiyar mahaifiyar Amir Khan ke nan. Kamar yadda ya bayyana da kansa, sabon dan wasan ya ce mahaifinsa ne ya ja ra’ayinsa har ya ji yana sha’awar ya fara sana’ar fim. Ya ce ya koyi wasu hikimomi na shirya fim ne daga mahaifinsa kafin ya mutu, domin kuwa ya yi aiki a karkashinsa a matsayin mai kula da gudanarwa a yayin shirya fina-finai.