Kanin gwamnan Nasarawa ya rasu

Bayan rasuwar dansa a watanni da suka gabata, ya rasa dan uwansa da sanyin safiyar Asabar.

Kanin gwamnan Nasarawa ya rasu

Kanin Gwamnan Jihar Nasarawa Abdullahi Sule, Labaran Sule ya rasu.

An ruwaito cewar dan uwan gwamnan ya rasu da sanyin safiyar ranar Asabar.

Musa Barau, mai taimaka wa gwamnan jihar ne, ya tabbatar da mutuwar Sule a wani sakon da ya wallafa a Facebook.

An gudanar da jana’izarsa a Fadar Sarkin Gudi da ke Karamar Hukumar Akwanga ta Jihar Nasarawa a yammacin ranar Asabar.

“Cikin bakin ciki muna sanar da rasuwar kanin Gwamnan Jihar Nasarawa Labaran Sule.

“An yi jana’izar marigayin a Fadar Sarkin Gudi da ke Karamar Hukumar Akwanga. Allah Ya jikansa Ya sa Aljanna Firdausi  ce makomarsa, amin ya rabbi,” in ji Barau.

Wannan na zuwa ne ‘yan watanni bayan gwamnan ya rasa dansa, Hassan Sule, wanda ya rasu a ranar 26 ga watan Janairu, 2023, bayan gajeriyar rashin lafiya.