Kannywood: Aminu Mu’azu ya zama shugaban MPEG

Kungiyar Masu Tace/Hada Hoton Finafinan Kannywood (MPEG) ta sauke shugabanninta

Kannywood: Aminu Mu’azu ya zama shugaban MPEG

Aminu Mu’azu S/Mainagge ya zama Shugaban Riko na Kungiyar Masu Tace/Hada Hoton Fina-finan Kannywood (MPEG) bayan an sauke shugabanninta.

Kungiyar ta ce daga yanzu kwamitin riko mai mutum uku karkashin jagorancin Aminu Mu’azu ne zai ci gaba da gudanar da ala’muranta.

Sakataren Kwamitin Rikon Kungiyar MPEG, Aliyu Mansur Yakasai, ta wata sanarwa ya ce, “Wannan matakin ya zama dole kuma ya yi daidai da manufar kungiyar don tabbatar da dorewarta da kuma cigabanta.

“Muna bai wa mambobinmu tabbacin bayar da muhimmanci ga tabbatar da hadin kai da fahimtar juna a duk abubuwan da za mu yi don kare kimarsu da mutuncinsu.”

Sabbin shugabannin rikon su ne:

  1. Aminu Muazu S/Mainagge – Shugaba
  2. Aliyu Mansur Yakasai – Magatakarda
  3. Jamilu Adam – Mamba

Ya ci gaba da cewa an sauke tsoffin shugabannin ne bayan kudurin neman hakan da aka gabatar, wanda ya samu samu amincewa a zamansu na ranar Lahadi, 30 ga watan Oktoba, 2022.

Ya ce yin hakan ya yi daidai da Sashe na 4 Karamin Sashe na 5 na Kundin Dokokin Kungiyar MPEG.

A cewarsa, zaman da ya gudana a gini mai lamba 108 Ahmad Baffa House, Ibahim Umar Street, Zoo Road, Kano ya samu halartar kashi biyu bisa uku na tsofaffin shugabanni da amintattu da masu ruwa da tsaki na MPEG.

Ya kuma sanar da alkawarin kwamitin rikon na gudanar da aikinsa bisa gaskiya da tsayawa kan daidai.

Don haka ya nemi hadin kai da addu’o’in mambobi wajen gudanar da aikinsu don cigaban sana’ar da ma ’yan kungiyar.