Kannywood: ‘Masu uwa a gindin murhu kawai ke samun gata a fim’
Maganar gaskiya idan har ba ka da wanda ya tsaya maka to sai a hankali, wanda kuma bai kamata ya zama haka ba.
Ahmed Bello, wanda aka fi sani a shirin ‘Dadin Kowa’ da Nazir, fitaccen dan wasan Hausa ne a Kannywood. A cikin wannan tattaunawar da Aminiya, ya bayyana yadda ya tsinci kansa a harkar fim da kuma yadda harkar ubangida ta yi tasiri a masana’antar ta Kannywood da sauran al’amura
Yaya aka yi ka tsinci kanka a masana’antar Kannywood?
Da farko ni na taso ne da sha’awar shiga harkokin siyasa ba na wasan kwaikwayo ko fina-finai ba. A lokacin ina kokarin neman aikin Kwastam. Da ban samu aikin ba sai na sake gwada shiga aikin DSS. A lokacin na bazama laluben aikin da zan yi ne kawai.
- Sarkin Lere ya riga mu gidan gaskiya
- Ganin ’yan bindiga ya fi sauki a kan ganin Buhari – Sheik Ahmad Gumi
Duk da cewa ni tun farko na taso a matsayin dan wasa ne don nakan yi wasan dabe. Ina daya daga cikin ’yan wasa yara da suka halarci wasan kalankuwa ta baje al’adu na kasa da aka yi a shekarar 1996.
Sai dai ban tsunduma cikin masana’antar fina-finai ba sai da na fara harkar koyar da rawa ga ‘yan wasa. Wani fitaccen mai furodusa mai suna Alhaji Aminu Gudun ne ya fara gayyata ta don yin aikin koyar da rawa a cikin fim dinsa mai suna ‘Miraj’, inda Ali Nuhu da Balaraba suka ja ragamar fim din. Wannan shi ne farkon lokacin da na yi aikin koyar da rawa a masana’antar Kannywood.
Fina-finan da ka fito a su kai nawa?
Na fito a cikin fina-finai da dama na Hausa da na Turanci. Daga cikin na Hausa akwai Kusufi da Shawagi da Buri da Tururi, a kamfanin FKD kuma na fito a fim din “Mansoor.”
A bangaren fina-finan Turanci kuma na fito a fim din “In Search of the King” da “The Right Choice” inda wasu fitattun ’yan wasa da suka hada da Eyinna sa Nancy Isime da Sola Sobowale da Segun Arinze suka taka rawa a ciki.
Idan muka waiwaya baya a yadda ka faro da kuma yadda kake a yanzu, ko ka samu gamsuwa?
Gaskiya ina cikin farin ciki sosai saboda na samu aikin yi. Ina gudanar da rayuwata babu wata tangarda kuma ina taimakawa iyalai na (duk da dai ba ni da aure har yanzu). Ba abin da zan ce sai dai Alhamdulillahi domin duk abokaina da wadanda muka yi makaranta tare duk wanda ya gan ni ya kan ce da ni sambarka.
Mene ne ra’ayinka a kan harkar ubangida a masana’antar Kannywood?
Maganar gaskiya ita ce masu uwa a gindin murhu ne kawai ake sakawa a fina-finai. Idan har ba ka da wanda ya tsaya maka to sai a hankali wanda kuma bai kamata ya zama haka ba. Ya kamata mu sauya yadda al’amuan ke tafiya. Idan har kana da baiwa da kuma kwarewa, to ko kana da ubangida ko ba ka da shi ya kamata a yi da kai.
Idan har za ka ce matsayinka na Furodusa ba za ka saka ni a fim din ka ba har sai na kawo wani ubangida a harkar to har yanzu ba a ci gaba ba ke nan. Ci gaba da hakan tamkar dakushe kamfaninka ne da kuma masana’antar baki daya.
Da yawa za ka ga tun kafin a je ga gwajin tantance ’yan wasa an riga an gama zabar wadanda za a saka fim wanda bai kamata ya zama haka ba. A kan kira tantance ’yan wasa don zakulo boyayyiyar baiwar da Allah Ya yi wa wasu wanda idan an mayar da hakan talla ne kawai da kururuwa to ya zama aikin kawai.
Me za ka ce a kan batun satar fasaha?
Kamar yadda kowa ya sani ne, yana daga cikin abin da ya kashe harkar fina-finai gaba daya a Najeriya; na Hausa da na Igbo da na Yarbanci. Ba yadda za a yi a matsayinka na Furodusa mai daukar nauyin shiri ka zuba kudinka ka yi fim sannan wani can dabam ya rika gurzawa yana sayarwa ba tare da sani ko izininka ba bayan ka gama shan rana da ruwa da iska don ganin ka fitar da abu mai kyau ka ci riba. Duk babu ruwansu da wahalhalun da ka sha su akwai abinda suka sani fim ya fito su je su kwafo su gurza su ci gaba da sayarwa wanda hakan bas hi da bambanci da fashi da makami.