Kannywood za ta iya gogayya da takwarorinta na duniya —Rukky Alim

Jarumar ta bayyana yadda ta tsinci kanta a masana’antar Kannywood.

Kannywood za ta iya gogayya da takwarorinta na duniya —Rukky Alim

Jaruma Rukky Alim

Rukayya Ahmad Aliyu, wadda aka fi sani da Rukky Alim jaruma ce a Masana’antar Kannywood da yanzu take jan zarenta bayan shigowarta masana’antar a bara.

A tattaunawarta da Aminiya, ta bayyana yadda ta fara fim da daukakarta da burinta a nan gaba.

Mene ne takaitaccen tarihinki?

Sunana Rukayya Ahmad Aliyu wadda aka fi sani da Rukky Alim a Masana’antar Kannywood. Ni ’yar asalin Jihar Taraba ce, daga Karamar Hukumar Jalingo, a wata unguwa da ake kira Unguwar Daji. Na yi karatun firamare da sakandare duk a garin Lau da ke Karamar Hukumar Lau a Jihar Taraba.

Daga baya na koma kasar Kamaru na ci gaba da zama. Ina can ne kuma Allah Ya yi dawowa ta Najeriya.

Yaya aka yi kika shiga harkar fim?

Zan iya cewa haka Allah Ya so kawai. Bayan na dawo Najeriya, sai na koma Jihar Kano da zama wajen wata yayata. Ina can ne Allah Ya hada ni da wata kawa, wadda take harkar fim.

Da muka shaku da ita, sai na bayyana mata cewa ina sha’awar harkar fim.

Sai ta ce za ta kai ni wajen masu harkar, idan za a bar ni in ci gaba. Sai na je gida na tambaya, kuma cikin ikon Allah aka ba ni dama, sai dai ’yan shawararwarin da aka ba ni. Sai ta kai ni na fara.

Ka ji yadda na shigo masana’antar. Da na shirya, sai muka je na samu jarumi kuma mawaki, Garzali Miko.

Na ce masa ina son harkar fim. Ya ce min babu damuwa. Lokacin ana kullen Kwarona ne, harkokin fim duk sun tsaya cak.

Ina cikin zaman jira ne sai wata rana ya kira ni a waya ya ce in zo mu yi aikin wani fim da zai yi mai suna Kaddarata.

Fim din Kaddarata shi ne fim dina na farko a Masana’antar Kannywood, wanda kuma shi ne sanadiyar da ake damawa da mu har yanzu. Kuma zuwa yanzu, sai dai godiya ga Allah.

Da bidiyon waka kika fara ko fim domin a wakokin aka fara saninki?

Gaskiya da fim na fara shiga harkar, kafin na fito a wakokin. Fim dina na farko shi ne Kaddarata kamar yadda na fada maka, daga baya sai muka fara wakoki da Garzalin. To amma an kalli wakokin sosai lokacin, sai mutane suke ganin kamar wakokin na fara.

Kin yi fina-finai nawa zuwa yanzu?

Ba su da yawa. Akwai In Da Rai na Garzali Miko, akwai In Da Ranka akwai Gwarama da Sanda da Haram da Asin da Asin na Adam A. Zango da Rana Dubu na Abubakar Bashir Maishadda da yanzu muke dauka da sauransu.

Wanne kika fi so a ciki?

Gaskiya babu wanda na fi so. Dukkansu ina so. Kusan dukkansu daya ne a wajena. Kuma kasancewar zan iya cewa na yi sa’a ne domin dukkansu manyan fina-finai ne.

Ganin yadda kika yi fice za a dauka ko kin yi shekaru da yawa ne, mene ne sirrin da kika haska a cikin kankanin lokaci?

Babu wani sirri. Gaskiya ban dade ba a harkar. Ba zan iya cewa don na fi wasu ba ne, domin muna da yawa. Amma watakila yanayi ne. Ka san kowa da yadda yake zuwa.

Watakila zuwan nawa ne ya zo a haka. Amma dai na san ina son mayar da hankali a kan aikin da nake yi, kuma ina girmama na gaba da ni, da sauran abokan aikina.

Duk rawar da aka ce in taka, ina bakin kokarina in fitar da abin da ake so, amma ko kadan ba don na fi sauran ba ne. A takaice dai haka Allah Ya so, kuma kowa da kaddararsa.

A cikin wakokin da kika fito fa, akwai wanda kika so?

Eh, to a wakoki zan iya cewa na fi son bidiyon wakar Butulci da na fito.

Me ya sa?

Ka san wani lokacin mutum yakan ji yana son wani abu a zuciyarsa. Na fi so ne kawai saboda yadda wakar ta zo. Ina jin dadin wakar.

Yaya kika samu sunan Alim?

Sunan gida ne.

Mene ne burinki a Masana’antar Kannnywood?

A dai yanzu ba ni da wani buri da ya rage. Na cika duk burina tunda dai tun farko ina sha’awar harkar, kuma na samu dama na shigo har na kai wannan matsayi. Gaskiya a yanzu ba ni da wani buri. Yanzu na samu suna da daukaka daidai gwargwado, ina godiya ga Allah da wadanda suka taimaka min.

Ba ki da burin zama forodusa ko darakta a nan gaba?

Gaskiya ba ni da wannan burin.

Za ki iya fitowa a fim din Nollywood?

Zan iya yi mana, amma sai na ga yanayin yadda labarin ya kama. Idan ba zai taba mutuncina ba, zan iya yi. Ka san tsarin Kudu daban da Arewa kuma kowane da irin rawa da sakon da suke isarwa. To idan yanayin fim din ya zo da tsarin da zan iya shiga ba tare da ya taba mutuncina da addini ba, zan shiga. Ai fim fim ne a ko’ina kuma ko ma da wane yare ne.

Su wane ne iyaye gidanki?

Ai ni iyayen gidan nawa da yawa suke, ba zan iya ware mutum daya ba.

Kin fito a Haram da Sanda, wadanda duk fina-finai ne na dabanci, kina sha’awar fim din daba ne?

Ba haka ba ne, ina fitowa a kowane irin fim. Fin dina na farko ai ba na daba ba ne. A Haram na fito a cikin ’yan dabar, a Sanda kuma a likita na fito. Fina-finan an shirya su ne domin jawo hankalin matasa a kan su daina harkokin daba.

A Sanda kamar akwai soyayya tsakaninki da Sanda din?

Ba soyayya ba ce. Ai ina da aure. Ina auren Garzali Miko, wanda shi kuma dan sanda ne da yake neman Sandan. Sanda ya taba taimako na, shi ne ni kuma da na gan shi ya ji rauni, na dauko shi na kawo shi gidana, na yi masa magani. Shi kuma mijina dama yana nemansa, sai ya zo ya gan shi a gidansa.

Wane kira kike da shi ga abokan sana’arki?

Ina kira gare su mu kara hada kanmu sannan mu zauna lafiya da junanmu baki daya. Mu rika girmama junanmu, mu girmama na gaba da mu. Idan aka samu hadin kai, masana’antar za ta fi cigaba. Kina kira ga masoya? Babu abin da zan ce sai dai godiya da fatan alheri. Ina ganin kauna sosai. Allah ya bar zumunci.