Kano: Abba ya ba da umarnin kama masu ‘dibar ganima’ a wuraren da ya yi rusau

Ya ce duk masu dibar kayan za su fuskanci fushin hukuma

Kano: Abba ya ba da umarnin kama masu ‘dibar ganima’ a wuraren da ya yi rusau

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya umarci Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar da ya fara kamawa tare da hukunta masu satar kayan gine-ginen da aka rushe da sunan ganima.

A daren Asabar ne dai Gwamnan ya jagoranci fara rushe wasu gine-gine da ya ce gwamnatin da ta gabata ta sayar da su ba bisa ka’ida ba.

To sai dai a duk lokacin da aka kammala rusau din a kan ga matasa suna far wa wajen suna dibar kayan ginin suna guduwa da su.

Amma a cewar wata sanarwa da Gwamnan ya fitar ta bakin Sakataren Yada Labaranshi, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya ce Gwamnan ya yi Allah wadai da abin da mutanen ke yi.

“A saboda haka, Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya umarci Kwamishinan ’Yan Sanda da ya gaggauta fara kamen irin wadannan mutanen tare da tabbatar da sun fuskanci fushin hukuma,” in ji sanarwar.

Daga nan sai ya bukaci al’ummar Jihar da su ci gaba harkokin kasuwancinsu kamar yadda suka saba, sannan su kai rahoton duk wadanda ke dibar kayan domin a dauki mataki a kansu.

Ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnatinsa ta kuduri aniyar karbo dukkan filayen gwamnati da aka gina ba bisa  da nufin farfado da martabar Jihar.

Tags