Kano: Abba ya miƙa buƙatar neman ƙarin kasafin N99bn

Za kashe N33.78bn daga wajen biyan albashi, N34bn ayyukan yau da kullum sai manyan ayyuka N30bn

Kano: Abba ya miƙa buƙatar neman ƙarin kasafin N99bn

Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya aike wa Majalisar Dokokin Jihar kuƙirin ƙarin kasafin kuɗi na Naira biliyan 99.22.

Abba ya shaida wa majalisar cewa yana neman amincewarta da ƙarin kasafin ne domin aiwatar da wasu muhimman ayyuka don inganta walwalar al’ummar Kano.

Takardar neman ƙarin kasafin wadda shugaban majalisar, Ismail Falgore, ya karanta, ta bayyana cewa Naira biliyan 33.78 daga cikin kuɗin za a kashe su ne wajen biyan albashi.

Ragowar su ne biliyan 34.5 da za kashe a kan ayyukan yau da kullum, sai manyan ayyuka da za a kashe biliyan N30.97 a kansu.

Bayan gabatar da takardar, Kwamishinan Kasafi da Tsare-tsare na Jihar Kano, Musa Shanono, ya bayyana cewa ƙarin kasafin zai ba wa gwamnatin jihar damar biyan sabon mafi ƙarancin albashi da ma sauran ayyukan cigaban al’umma, musamman a ɓangarorin ilimi da kiwon lafiya.

Ya shaida wa ’yan jarida cewa kasafin 2024 na jihar na da majalisar ta fara amincewa da shi Naira biliyan N437.34 ne.

Don haka idan aka haɗa da ƙarin da aka kawo, jimilla ya kama Naira biliyan 536.56.

HOTUNA: Ɗaurin auren ’yar Kwankwaso ya haɗa Atiku, Obasanjo, Kashim Shettima da manyan ’yan siyasa a Kano

HOTUNA: An soma kaɗa ƙuri’a a Zaɓen Ondo

Mai hannu ɗaya da ke sana’ar faskare

Dole talauci ya yi katutu a Arewa!