Kano: Abba ya nada Darakta-Janar kan tallace-tallace a titi
Gwamann Jihar Kano Abba Kabir Kano ya nada Darakta-Janar mai kula da tallace-tallace a kan tituna a cikin sabbin jami’an gwamnatinsa
Gwamann Jihar Kano, Abba Kabir Kano, ya nada Darakta-Janar mai kula da tallace-tallace a kan titi a cikin sabbin jami’an gwamnatinsa.
Surajo Imam Dala shi ne sabon Darakta-Janar mai kula da tallace-tallace a kan titi da sana’o’in cikin gida kuma sabbin nade-naden sun fara aiki ne nan take.
Sabbin mukamin sun hada da daga matsayin sakataren yada labaransa, Sanusi Bature Dawakin Tofa, zuwa Darakta-Janar na yada labarai.
Daraktan yada labran gidan gwamantin jihar, Aliyu Yusuf, ya sanar a ranar Alhamis cewa gwamnan ya nada sabbin shugabannin bakwai da kuma masu ba shi shawara na musamman guda 13.
- Harin Mauludin Kaduna ba kuskure ba ne —Sheikh Gumi
- Kotu ta tilasta gwamnatin Kano biyan diyyar rusau
Ya bayyana cewa daga yanzu, Hon. Rabi’u Saleh Gwarzo shi ne Kwamishina I na hukumr SUBEB; Injiniya Sarki Ahmad shi ne Darakta-Janar na shirin shirin samar da hanyoyi a yankunan karkara.
Dokta Dahiru Saleh Muhammad, Babban-Sakatare Hukumar Makarantun Kimiyya; Abubakar Adamu Rano, Mataimakin Manajan Daraktta, Radio Kano; Hajiya Hauwa Isah Ibrahim, Mataimakiyar Manajin Daraktta, ARTV sai Dokta Gaddafi Sani Shehu Mataimakin Manajan Darakta, KHEDCO.