Kano: Abba ya nada sabbin sarakuna uku
Abba ya sake nada Sarkin Gaya da aka tube tare sabbin sarakunan Karaye da Rano
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya nada sabbin sarakuna masu daraja ta biyu guda uku.
A cikin daren Talata gwamnan ya mika takardun fara aiki ga sabbin sarakunan na masarautun na Gaya, Karaye, da kuma Rano.
Sabbin sarakunan su ne Alhaji Muhammad Maharaz Karaye, a matsayin Sarkin Karaye, wanda kafin yanzu shi ne Hakimin Rogo.
Sai Hakimin Bunkure, Alhaji Muhammad Isa Umar, a matsayin sabon Sarkin Rano.
- DAGA LARABA: Shin Tallafin Abinci Ne Zai Magance Damuwar Talakan Najeriya?
- Sanatoci na shirin tsige Ndume kan sukar Tinubu
Na uku shi ne Sarkin Gaya, Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir, wanda gwamnatin jihar ta tsige a watan Mayu tare da takwarorinsa na masarautun Bauchi da Rano da Kano da kuma Karaye da aka rushe.
Sanarwar nadin da kakakin gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a cikin dare ta ce, sabanin sauran sarakunan, Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir Gaya, ya rungumi kaddamar tare da ba da tabbacin yin aiki a duk matsayin da aka sanya shi.
Sanarwar ta ce nadin sabbin sarakunan ya fara aiki nan take.
Gwamnan ya kuma umarci sarakunan masu daraja ta biyu da su kasance masu wanzar da zaman lafiya da hadin kan al’umma da kuma raya al’adu.